Daga Idris Shehu
Kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta jihar Bauchi (Correspondents’ Chapel) a Litinin din ta cimma matsayar dakatar da daukan labaran ofishin mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Sanata Baba Tela bisa wulakanta su a bakin aiki.
A wani sanarwar manema labarai da sakataren kungiyar, Mr Samuel Luka ya fitar a Litinin din nan, ya shaida cewar daukan matakin ya biyo bayan halin rashin mutuntawa ne da mataimakin gwamnan ya nuna a ofishinsa.
“Daukar wannan matakin ya biyo bayan lamarin da ya faru a ofishin mataimakin gwamnan ne wanda ya nemi ‘yan jaridan da aka gayyata domin daukan labari da su fice masa daga wurin zaman ba tare da amfani da kalaman mutuntawa ba.”
“Kalaman da ya yi amfani da su ba su mana dadi ba, ya dace kamar yadda aka gayyace mu, ya mutunta domin mu bakin aikinmu ne na hidimta wa al’umma,” inji sanarwar.
Luka ya shaida cewar a wani zaman gaggawa da kungiyar ta kira a Litinin din nan, mambobin kungiyar sun dauki matakin daina kula da harkokin labaran mataimakin gwamnan har zuwa daukan mataki na gaba.
Chapel din ta nuna damuwarta da bacin ranta bisa rashin samun kyakkyawar hadin kai a tsakanin ofishin mataimakin gwamnan da ‘yan jarida.
Daya daga cikin ‘yan jaridan da lamarin ya faru a kan idonsu, ya shaida mana cewar mataimakin gwamnan bai yi amfani da kalamai na mutuntawa a garesu ba, “Mun dauka hakan da ya mana a matsayin wulakanci. Mun je ofishinsa ne bisa gayyata domin daukan rahotonni da zimmar sanar da duniya halin da ake ciki.
“Bayan mun zauna a cikin dakin taron, inda wasu masu ruwa da tsaki su ma suka zo suka zauna. Fitowar mataimakin gwamna zuwa dakin taron ke da wuya kawai sai ya ce a fita masa daga wajen. Mun dauka in ma ganawa ce za su yi, sai ya ce a dan jirasu a waje daga baya zai gana da ‘yan jarida,” ya ce sam ba su ji dadin hakan ba.