Wasu ’yan kasuwa a jihar Jigawa sun rufe kasuwancinsu saboda karancin sabbin takardun kudin Naira, Daily Post ta rawaito.
Hakan ya biyo bayan sanarwar da babban bankin Najeriya CBN ya bayar na cewa ranar 31 ga watan Janairu ya rage wa’adin daina amfani da tsofaffin kudaden Naira a fadin kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kano Ta Karawa Ma’aikata 117 Matsayi, Ta Kori Guda Biyu
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta ruwaito cewa CBN ya sanya ranar 31 ga watan Junairu 2023 a matsayin wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kudi na N200, N500, da kuma N1000 bayan ya sake canza wasu sabbi a ranar 15 ga watan Disambar shekarar 2022.
Da suke mayar da martani dangane da ranar da babban bankin na CBN ya sanyawa hannu, wasu ‘yan kasuwa a Dutse, babban birnin jihar, sun ce ba su da wani zabi da ya wuce su rufe kasuwancinsu har sai an samu sabbin takardun Naira.
Wani dan kasuwa da ke da kantin sayar da kayayyaki a Yelwawa Quaters a cikin birnin Dutse, Malam Musa, ya ce ya rufe shagonsa ne saboda rashin samun sabbin takardun kudi na Naira.
“Na kasance ina sayar da kayan kusan N200,000 a kowace rana amma da kyar na samu Naira 10,000 sabbin takardun kudi, kuma duk lokacin da na karbi tsohon na kan sha wahala wajen canza shi a bankina saboda dogayen layukan da ake yi,” inji shi.
“Don haka don kasancewa a gefen mafi aminci na rufe kasuwancina har sai bayan an sami sabbin takardun kudin Naira.”
Haka kuma, wata mai sayar da kosai a kusa da Gida Dubu a Dutse, Bintu Samuel, ta ce ta rufe kasuwancin ta har sai sabbin takardun kudi sun fara zagawa a hannun Jama’a.
“Duk wanda ya sayi kosaina yana ba ni tsofaffin takardun kudin, kuma lokacin da na ɗauka don siyan kayana, sun ƙi shi don haka in rufe har sai bayan an fara fitar da sabbin takardun naira,” in ji ta.
Wakilinmu daya zagaya wasu bankunan inda ya lura cewa kwastomomi sun hau kan layi tun karfe 7 na safiyar Laraba domin ajiye tsofaffin takardun kudin su, wasu kuma suna ciro sabbin kudi a na’urar ATM.
Idris Musa daya daga cikin kwastomomin daya daga cikin bankunan kasuwanci ya ce ya kwashe sama da sa’o’i 24 a cikin jerin gwano kafin ya ajiye tsoffin takardunsa.
Ya bayyana cewa jinkirin ya faru ne saboda mutane suna kawo tsofaffin takardun kudi a cikin manyan jakunkuna, kuma ana daukar lokaci mai yawa kafin mai karbar kudi ya gama kirga kudin.
Har ila yau, Malam Usman a Dutse ya ce ya kwashe kimanin sa’o’i 8 a layin ATM kafin ya cire Naira 20,000 na sabbin takardun kudi na Naira.
Sai dai sun ce suna kira ga babban bankin kasa da na kasuwanci da su yi la’akari da irin wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke ciki da kuma samar da mafita ga matsalolin.
Majiyar mu ta kuma samu labarin cewa lamarin na iya kara tabarbarewa nan ba da dadewa ba saboda biyan albashin da gwamnatin jihar ta yi a ranar 25 ga watan Janairun 2023.
A wani labarin kuma, Gwaman Zulum Ya Tarbi ‘Yan Gudun Hijirar Najeriya Sama Da 1, 000 Daga Kamaru
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum a ranar Talata ya karbi kashin na biyu na karin ‘yan gudun hijirar Najeriya 855 da aka dawo da su gida daga makwabciyar kasar Kamaru. Kammar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Jami’an kasar Kamaru karkashin jagorancin gwamnan yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru, Minjinyawa Bakari ne suka mika masa ‘yan gudun hijirar a wani taron bankwana da aka yi a birnin Maroua.