Majalisar wakilai, a ranar Talata, ta umurci manyan hafsoshin tsaro da kuma dukkanin hukumomin leken asiri da sauran masu ruwa da tsaki su bayyana a gabanta a ranar Laraba, kamar yadda Tribune Online ta rawaito.
Shugaban kwamitin rikon kwarya da ke bin diddigin ayyukan yi da kuma karkatar da tsarin biyan albashin ma’aikata (IPPIS) na hukumomin gwamnatin tarayya, Hon. Yusuf Gagdi, ya mika wannan umarni a Abuja.
KARANTA WANNAN: Har Yanzu Bamu Fara Kwashe ‘Yan Kasar Mu Daga Jamhuriyar Nijar Ba — Amurka
Hon. Gagdi wanda ya nuna rashin jin dadinsa kan rashin zuwan duk da cewa an gayyace su yadda ya kamata, ya ce: “Bari in fadi haka ga dukkan hukumomin da muka gayyata, ina ganin muna bukatar mu karanta sunayensu karara a nan.
“Su ne Nigerian Communications Satellite Limited, NBC, NCC, Nigerian Post Services, Nigerian frequency management Council, Galaxy Backbone, National Identity Management Commission, Nigerian Correctional Service, NIS, Fire Service, NPF.
Sauran sune, Hukumar Leken Asiri ta Tsaro, Hukumar Tsaro ta SSS, Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Sashin Leken Asiri da Kudade, Sojojin Najeriya, Sojojin Sama, Sojojin Ruwa na Najeriya dole ne su bayyana a gobe Laraba tunda sun kasa bayyana a yau Talata, Wannan shi ne hukuncin kwamitin,” in ji Hon Gagdi.
A nata jawabin, Akanta Janar ta kasa (AGF) wacce ita ma ta musanta zargin cewa ofishinta na yin rajistar ma’aikatan bogi ne domin biyan bukatun kashin kai, ta bayyana cewa ofishin nata na aiki tukuru wajen kamo ma’aikatan bogi da suka kasance a cikin tsarin a da. Gabatar da Haɗin Kan Biyan Kuɗi da Tsarin Bayanan Ma’aikata.
Ta ce: “Bayan na fahimci cewa wannan tsari ne da ya kamata a yi nazari a kai, a kan aikina, sai na gamu da matsaloli da dama a kan IPPIS wanda hakan ya sanya na tsara masu ruwa da tsaki da duk masu ba da sabis a kusa da IPPIS, sun zo sun gabatar da jawabi,da aka yi musu tambayoyi.
“Taron da masu ruwa da tsaki ya gudana na tsawon makonni biyu inda aka tsara dukkan masu ba da sabis a kowace rana kuma sun zo da hannayensu na fasaha yayin da kungiyar kwararru ta OAGF kuma ta kasance a kasa inda muke tattaunawa kan batutuwan da suka shafi tsarin.
“Yanzu na samu rahoton wucin gadi na wannan taro, wanda muke duba don ganin yadda muka magance dukkan matsalolin da suka taso daga wannan aiki domin ba mu damar daukar karin matakai kan gudanar da IPPIS.”
Ta ce 640 ne kawai daga cikin sama da hukumomi 900 na Gwamnatin Tarayya aka kama a IPPIS.
“Ya zuwa yau muna da MDA 640 da suka yi rajista a IPPIS, wadanda suka yi rajista a IPPIS, saboda akwai wadanda ba sa cikin IPPIS kamar dukkanin hukumomin tsaro, kamfanoni mallakar gwamnatin tarayya da ke samar da kudaden shiga, ba sa cikin IPPIS.
A wani labarin kuma, Zaben Shugaban Kasa: Ya Kamata Atiku Ya Yi Ritaya Daga Siyasa – Adeyanju
Dan gwagwarmayar zamantakewar al’umma, Deji Adeyanju, ya shawarci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da ya yi ritaya daga siyasa.
A wani sako daya wallafa a shafin sa na tweeter, Adeyanju ya rubuta cewa: “Atiku ya tabbata ya ci zaben amma bai san yadda zai tabbatar da hakan ba. Kawai yana jaddada kansa ba don komai ba.