Asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce kimanin ‘yan Najeriya miliyan 17.7 ne ke fama da yunwa, kuma adadin na iya karuwa zuwa miliyan 25.
Jami’ar kula da abinci mai gina jiki ta Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), Nkeiruka Enwelum, ta bayyana hakan kwanan nan yayin wata tattaunawa ta kwanaki biyu da kafafen yada labarai suka yi kan bayar da tallafin abinci mai gina jiki a Najeriya.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Kano Ta Fara Shirin Kula da Haihuwa Kyauta, Asibitocin Tafi da Gidanka
Hukumar kare hakkin yara (CRIB) na Ma’aikatar Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a ta Tarayya ta shirya tare da hadin gwiwar UNICEF.
A cewarta, Legas, Borno, Katsina da kuma Kano ne suka fi kowacce yawan mutanen da ke fama da karancin abinci a kasar, duk da cewa ta koka da yadda ake fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki a Najeriya.
Kasar, in ji ta, mai yiyuwa ne ta cimma burin ci gaba mai dorewa (SDG) kan shayar da jarirai nonon uwa ta shekarar 2030 amma ta ci gaba da kasancewa kan gaba wajen cimma SDG2 kan rashin yunwa.
A halin yanzu, Enwelum ya tabbatar da cewa, kimanin yara miliyan 35 a Najeriya na fama da tamowa, inda kasar ke da adadin yaran da cutar ta fi kamari a Afirka, sannan kuma ta biyu a duniya.
“Kusan yara miliyan 35 na yara ‘yan kasa da shekaru biyar a Najeriya na fama da tamowa. Kuma daga cikin wannan, miliyan 12 na kange,” inji ta.
Ta kuma danganta matsalar karancin abinci mai gina jiki a kasar nan da talauci, jahilci, da rashin wadataccen kasafi don samar da abinci mai gina jiki.
Tun da farko a nasa jawabin, kwararre kan harkokin sadarwa na UNICEF, Geoffrey Njoku, ya koka da cewa gwamnatocin tarayya da na jihohi ba sa kashe isassun kudade don magance karuwar matsalar karancin abinci mai gina jiki a kasar.
Daga nan sai ya kara da cewa adadin karancin abinci mai gina jiki a Najeriya ya yi yawa; don haka akwai bukatar a toshe gibin kudade ta hanyar tattara albarkatun cikin gida da kuma kara wayar da kan jama’a daga kafafen yada labarai.
A wani labarin kuma, Kotu Ta Bayyana Ministan Tinubu a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Sanata, Ta Kori Na PDP
Kotun sauraren kararrakin zabe ta bayyana Ministan Kwadago da samar da Ayyukan yi, Simon Lalong a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Filato ta Kudu
Alkalin kotun ya ce ba a tantance dan takarar PDP ba, don haka ya bayyana ministan na Jam’iyyar APC
A cewar alkalan, har zuwa lokacin tantancewar, jam’iyyar PDP ba ta da wani tsari mai inganci a jihar
Kotun sauraren kararrakin zabe ta Majalisar Dokoki ta kasa da ke Jos, Jihar Filato, ta bayyana Ministan Kwadago da samar da Ayyukan yi, Simon Lalong a matsayin wanda ya lashe zaben Sanatan Filato ta Kudu.
Shugaban kwamitin mai mutane uku,kar kashin jagorancin Mai shari’a Mahmoud Tukur, wanda ya bayyana hukuncin a ranar Litinin, ya bayyana cewa an yi asarar kuri’un da dan takarar jam’iyyar PDP, Napoleon Bali ya samu a zaben da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu.