Kusan ‘yan Najeriya miliyan 25 na fuskantar barazanar yunwa tsakanin watan Yuni da Agustan shwkarar 2023, idan ba a dauki matakin gaggawa ba, a cewar wani kididdigar bincike da Cadre Harmonisé, gwamnati da Majalisar Dinkin Duniya ke jagorantar kan abinci mai gina jiki sau biyu a shekara.
Punch ta ruwaito cewa, Wannan dai wani kari ne da aka yi kiyasin cewa mutane miliyan 17 ne ke fuskantar barazanar karancin abinci a halin yanzu.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Najeriya Sun Fi Shiga Halin Kunci A Yau Fiye Da 2015 – Atiku
Wata sanarwar da aka wallafa a shafin yanar gizon UNICEF ta bayyana cewa ci gaba da tashe-tashen hankula, sauyin yanayi, hauhawar farashin kayayyaki, da hauhawar farashin kayan abinci, su ne ke haifar da wannan mummunan yanayi.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce daga cikin mutane miliyan 17 da ke fama da karancin abinci a halin yanzu, miliyan uku na cikin jihohin arewa maso gabas, inda ta kara da cewa, idan ba a dauki matakin gaggawa ba, ana sa ran adadin zai karu da miliyan 4.4 a lokacin rani.
Rahoton ya ci gaba da cewa, kusan kaso shida daga cikin miliyan 17 da ke fama da karancin abinci a Najeriya a yau yara ne ‘yan kasa da shekaru biyar da ke zaune a jihohin Borno, Adamawa, Yobe, Sokoto, Katsina, da Zamfara.
A wani labari kuma, Peter Obi Zai Gana Da Malaman Addini da Sarakunan Gargajiya A Kaduna
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, zai gana da malaman addini a Kudancin Kaduna tare da ziyartar fadar sarakunan gargajiya.
Haka kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour zai gudanar da wani taro a filin wasa na Ahmadu Bello sannan kuma zai gana da daliban cibiyoyi da masu kishin jam’iyyar domin nuna goyon baya ga jam’iyyarsa.