Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party Peter Obi ya koka kan yadda ake ci gaba da fuskantar matsin rayuwa a wannan lokaci, da yan Najeriya ke gwammace kida da karatu ta fuskar rayuwa.
Peter Obi a wajen wani taron kan harkar Kasuwanci da aka shirya a Jihar Legas, ya nake kolin halin da yan Najeriya ke ciki, da kuma irin rawar da zai taka wajen kawo musu mafita.
KARANTA ANAN: INEC Ta Ja Kunnen Jam’iyyu, Gabanin Fara Yaƙin Neman Zaɓe
A cewar Peter Obi, akwai yan Najeriya sama da Miliyan 100 dake fama da kangin talauci, daidai lokacin da gwamnati ta APC ta gaza aiwatar musu da komai.
A cewarsa shi dan kasuwa ne, kuma ya kware a wannan fagen, don haka akwai dabaru masu yawa da zai yi amfani dasu wajen shawo kan matsalar, tare da ribatar harajin da ya kamata ace ana samarwa a kowace rana a Najeriya.
A wani labarin kuma: An Gargaɗi Tinubu Da APC Kan Amfani Da Kuɗi Wajen Raba Kan Kiristoci
An gargadi jam’iyyar APC mai mulkin kasa, da dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu, da kada su haifar da rabuwar Kawuna Tsakanin Kiristoci ta hanyar amfani da kudi.
Gargadin ya fito ne a cikin wata sanarwa da kungiyar dattawan kiristoci ta jihohin Arewa ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Oyinehi Inalegwu, a ranar Talata.