Mataimakin shugaban Majalisar datijjan tarayya Sanata Ovie Omo-Agege ya gargadi jam’iyyar APC mai mulki a ksar nan da kada ta kuskura t5a maimaita kuskuren da PDP ta yi a baya.
Omo-agege yana wanna jan kunne a yayin babban taron nazarinkan kundin tsarin jam’iyar APC wanda ya gudana a birni Asaba.
Ya ce ko shakku babu ko da gigin wasa yan najeriya ba za su zabi APC indai har wadannda ke kan karagar mulki yanzu suka kasa cika alkawuran suka dauka.
“Mun kafa tarihi a kasar nan, karon farko jam’iyyar APC ce ta taba tunbuke jam’iyya mai ci a kan karagar mulki a rtarihin kasr nan”
“Yan uwa na yan jam’iyya, ku tuna fa a baya PDP ta ce za ta ci gaba da kasancewa a kan mulki har na tsawon shekra sittin. amma menene ya biyo baya, yan kasa sun yi kukan kura inda suka kawar da ita”
“Menene ya kamata mu yi kamata ya yi mu dauki darasi”
Daga nan sai ya ja hankalin kwmaitin dake nazaari kan kudnin tsarin mulkin da su yi la’akari da dukkanin bangarori dake bada gudumawa wa jam’iyyar.