Hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta bayyana cewa wasu rukunin ‘yan Najeriya 180 da suka fake a kasar Libya sun so filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
Yan Najeriya da suka fake dai an taimaka musu ne zuwa kasar ta hanyar shirin Tarayyar Turai na musamman wanda hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya (IOM) ke aiwatarwa.
Mutanen da suka dawo sun isa tashar Cargo na MMIA a daren jiya Talata a cikin jirgin Al Buraq Air Boeing 737-8GK mai lamba BRQ UZ 189/190 wanda ya taso daga filin jirgin saman Mtiga na kasar Libya.
Alkaluman wadanda aka dawo da su sun nuna cewa sun hada da manya mata 74, yara mata 14 da jarirai mata shida da kuma manya maza 64, yara maza 12 da jarirai maza 10.
Ana ajiye mutanen da suka dawo na tsawon kwanaki bakwai na wajabta kafin a ba su izinin zuwa wuraren nasu ga wadanda ba su da wata matsala ta rashin lafiya.
Ko’odinetan hukumar NEMA a Legas, Mista Ibrahim Farinloye, ya ce: “A yayin da ake kebe mutanen, za a horar da ‘yan gudun hijirar kan sana’o’i daban-daban da kuma kananan dabarun kasuwanci”
Sauran hukumomin da suka shiga ayyukan sun hada da NAPTIP, hukumar kula da ‘yan gudun hijira da bakin haure, hukumar shige da fice ta Najeriya, da dai sauransu.