Mallakar mota na daga cikin jerin nasarorin da mafi yawan ‘yan Nijeriya ke ganin sun samu,yayinda ake biki a gidaje idan wani ya sayi mota a wasu yankunan.
Iyaye da ’yan uwa da abokan arziki su taru wajen yin addu’o’i ga Allah daban-daban domin ceto ran mai motar da ita kanta motar.
Sai dai kuma halin da kasar ke ciki a yanzu ya sanya wasu masu motoci su sayar da motocinsu, a kalla, don ciyar da iyalansu yadda ya kamata.
Karanta nanFG ta Shirya Samar da Rundunar ‘Yan Sanda Ta Musamman Kan Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba
Economy & Lifestyle ta gano cewa hatta masu son mota a yanzu suna sayen na Najeriya da aka yi amfani da su, maimakon wadanda ake shigo da su cikin kasar, wadanda aka fi sani da motocin Tokunbo.
A yau, mallakar mota an daina kidaya shi a matsayin nasara sakamakon yada sayen motar ya zama larura ga wasu.
Wadanda ke siyan motocin da aka yi amfani da su a Najeriya, bincike ya nuna, ba su taba yin hakan don jin dadi ba amma galibi don safarar kasuwanci kamar Uber, Bolt da inDrive, da sauransu.
Mista Salami Shotunde, wani ma’aikaci, ya ce sai da ya sayar da motarsa bayan ya ajiye ta na kwanaki a gidansa, saboda gazawar da ya yi mata a wannan karin farashin man fetur.
Na yi bakin ciki sosai a halin yanzu da yawancin ‘yan Najeriya ke rayuwa cikin matsi kamar dai ni,domin sai da na siyar da motata sannan na samu na sayi abinci.
Dole ne in sayar da samfurin Toyota Camry dina, 2006, bayan ajiye shi a gida na tsawon watanni.
Sayen mai yana da tsada kuma kasuwanci ba ya tafiya ko kadan. Abu mafi mahimmanci a yanzu shine kasancewa cikin koshin lafiya, kuma ciyarwa shine babban sashi a ciki.
Don ciyar da iyalina, dole ne in sayar da motata inji shi.
A wani labarin kumaFG Zata Kara Yawan Danyen Man Data Ke Hakowa Zuwa bdp 2m
Har ila yau, Mista Olamide Balogun, wani dan kasuwa, wanda ya sayi mota kirar Toyota Sienna, ya ce na sayi mota kirar Toyota Sienna da Najeriya ke amfani da ita, kwanakin baya a kan Naira miliyan 3.8.
Abin da mutane ke siya ke nan, domin waɗannan motocin Tokunbo suna da tsada sosai.
A halin yanzu, ban saya don jin daɗi ba amma don kasuwancin sufuri. Na yi mamakin bacin ran wanda na sayi motar a hannunsa wanda ya gaya min cewar ya sayar da motar don kawai ya ciyar da iyalinsa.