- Rundunar ‘yan sandan ta cafke shugaban kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasa Tajudeen Baruwa
- Hakan ya biyo bayan wani samame da jami’an ‘yan sanda da DSS suka kai a sakatariyar kungiyar ta kasa da ke Abuja
- Simanen ya zone lokacin da kungiyar take tsaka da shirye-shiryen kaddamarwa da rantsar da sabbin zababbun ‘yan majalisar gudanarwa ta kasa
Rundunar ‘yan sandan ta kame shugaban kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasa Tajudeen Baruwa da wasu jami’an kungiyar uku, Punch ta rawaito.
Hakan ya biyo bayan wani samame da aka kai a sakatariyar kungiyar ta kasa da ke Garki 2 Abuja a yammacin ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN: Gwamnan APC Ya Bayyana Sabuwar Abokiyar Takararsa, Ya Watsar da Mataimakinsa
‘Yan sanda dauke da makamai da jami’an DSS ne suka mamaye sakatariyar inda suka bukaci daukacin mutanen da su bar ginin da aka rufe.
Mataimakin shugaban kungiyar, Mista Isa Ore, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Asabar.
Isa, wanda ya bayyana kaduwarsa da faruwar lamarin, ya ce ba a ba su wani dalilin daukar matakin ba.
Ya ce kungiyar na shirye-shiryen kaddamarwa da rantsar da sabbin zababbun ‘yan majalisar gudanarwa ta kasa ne a lokacin da ‘yan sanda suka isa wurin suka umarci ma’aikatan da su fice tare da rufe harabar.
Ya ce, “Mun yi matukar kaduwa da muka ga jami’an ‘yan sanda sun kulle sakatariyar mu ba tare da ba mu wani dalili ba.
“A yau Asabar muna shirye-shiryen kaddamar da sabbin zababbun ‘yan majalisar gudanarwa na kasa, amma sai muka ga ‘yan sanda, sai suka ce mu bar harabar. Sun ce umarni ne daga sama suka tsare shugabanmu da sauran shugabannin a ofishin ‘yan sanda na Wuse.
“Na kira kwamishinan ‘yan sanda na FCT amma ya ce ba ya gari”
Ya bayyana sunayen wasu jami’an da aka kama a matsayin Babban Sakatare, Anthony Asogwa Chukudi, Olayi Odion, National Trustee, Babban Mataimakin Sakatare, Abdulrasak Yemi.
Yanzu haka dai jami’an na tsare a sashin Wuse Zone 3.
A wani labarin kuma, Hawaye Sun Kwaranya: Ambasadan Najeriya A Faransa Ya Kwanta Dama
Ma’aikatar harkokin wajen tarayyar Najeriya ta sanar da rasuwar Ambasadan Najeriya a Faransa, Kayode Laro.
Ma’aikatar, a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, mai dauke da sa hannun kakakinta Misis Francisca Omayuli, ta ce Laro ya rasu ne a ranar Juma’ar da ta gabata a birnin Paris na kasar Faransa bayan ya sha fama da rashin lafiya.