Hukumar Kula da Rarraba Wutar Lantarki ta Kano (KEDCO) ta bayyana farin cikinta kan yadda jami’an ‘yan sanda suka kama wani mutum daya kware wajen iya lalata wayoyin wutar lantarki a karamar hukumar Kaugama ta jihar Jigawa.
A cewar hukumar, an kama wanda ake zargin kuma an gurfanar da shi a gaban wata kotun majistare tare da tuhumarsa da lalatawa da kuma satar wayoyin wutar lantarki daga cibiyoyin kamfanin KEDCO.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari Ya Kuduri Aniyar Gudanar Da Sahihin Zabe A Najeriya – Fadar Shugaban Kasa
Rundunar ‘yan sandan ta samu nasarar cafke Hussaini Ibrahim wanda yanzu haka yake tsare yayin da ake tsare da Sulaiman Salisu.
Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa, mataimakin babban Manaja na Kamfanin mai kula da sadarwa na KEDCO, Ibrahim Sani Shawai, ya ce, “Mun himmatu wajen kare aikin mu ta hanyar hadin gwiwa da hukumomin tsaro da shugabannin al’umma.
Har ila yau, muna gargadin mazauna garin da su nisanci duk wani shigarwa don kare lafiyarsu da isar da sabis mai inganci ga abokan cinikinmu da yawa.
“Muna kira ga al’ummarmu da su taimaka wajen kai rahoton duk wani yunkuri ko ake zargi na sata da barnatar da kayan aikin KEDCO ga jami’an tsaro ko kuma ofisoshin KEDCO mafi kusa don daukar mataki.”
A wani labarin kuma, Addu’ar Amurka Muke Bukata Ba Tsorata Yan Najeriya Ba, Ministan Buhari
Ministan ya ce sanarwar ta’addancin ya kara jefa jama’a cikin rudani tare da tsorata ‘yan Najeriya har suka kasa daukar matakin da ya dace.
Sai dai ya ce barazanar ba ta yi muni ba, yana mai tabbatar da cewa gwamnati ta hanyar hukumomin tsaro da na leken asiri ne ke kan gaba a lamarin.