By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke wata matar aure mai suna Ramota Bello bisa zargin kashe mijinta, Bello Saliu.
An kama wadda ake zargin ne a ranar Litinin, kwanaki tara bayan ta yi wa mijinta wanka da ruwan zafi wanda ya kai ga mutuwarsa washegari.
An ce wani kanin mamacin ne ya kai rahoton faruwar lamarin a hedikwatar Lafenwa dake Abeokuta.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Rahotanni sun ce wacce ake zargin ta kashe mijinta ne da ruwan zafi bayan ta zuba masa a lokacin da yake barci.
A cewar Oyeyemi, lamarin ya faru ne a ranar 12 ga watan Fabrairun 2022, bayan da wadda ake zargin ta samu ‘yar karamar rashin jituwa da mijinta. wanda hakan yasa ta tafasa ruwa a tukunya ta zuba wa mijinta wanda a lokacin yana barci, inda hakan ya jawo masa mummunan rauni a jiki.
Oyeyemi ya kara da cewa, “An garzaya da wanda iftila’in ya afkawa zuwa asibiti domin yi masa magani amma ya mutu a ranar 13 ga watan Fabrairun 2022 a lokacin da yake karbar magani.
“Wanda ake zargin, bayan ta fahimci girman laifin data aikata, tunda ga lokacin ta yi batan dabo.
“Ba a kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda ba sai ranar 21 ga watan Fabrairun 2022, lokacin da aka ga wacce ake zargin a maboyar ta.
“Bayan rahoton, DPO na Lafenwa, CSP Kayode Shadrach, ya yi gaggawar yin cikakken bayani ga jami’an bincikensa zuwa wurin da aka kama wanda ake zargin.”
A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin cikin gaggawa zuwa ga sashen binciken laifuka da leken asiri na jihar domin gudanar da bincike mai zurfi da kuma tuhumar ta.
Comments 1