‘Yan sanda a Zamfara sun ceto mata shida da dan shekara daya da aka yi garkuwa da su. Kamar yadda Daily Nagerian ta ruwaito.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Muhammad Shehu, ya bayyana haka a garin Gusau a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya ce masu garkuwa da mutane sun kama mutanen a kauyen Kadamutsa da ke karamar hukumar Zurmi a ranar 24 ga watan Nuwamban shekarar nan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dandazon Kungiyoyi Magoya Bayan Atiku Sun Sauya Sheka Zuwa APC
Sai dai ‘yan sanda sun ceto mutane bakwan a hanyar Zurmi zuwa Jibia a ranar Asabar 26 ga watan Nuwamba.
Dimokuradiyya ta nakalto cewa, Sufeto ya kara da cewa, an yi nasarar ceto mutanen ne tare da taimakon kungiyoyin sa kai na yankin da kuma rahoton sirri da ‘yan sanda suka samu.
“Jami’an ‘yan sanda sun yi tattaki zuwa yankin inda aka gudanar da aikin ceto a kan babbar hanyar tarayya ta Zurmi zuwa Jibiya inda aka ceto duk wadanda abin ya shafa ba tare da wata matsala ba.
“An kai wadanda aka ceto zuwa asibiti domin duba lafiyarsu, ‘yan sanda sun dauki bayanansu sannan kuma aka sada ssu da iyalansu,” in ji Shehu.
Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda, Kolo Yusuf ya yabawa jami’an ‘yan sandan bisa nasarar ceto mutanen.
Mista Yusuf ya kuma taya wadanda lamarin ya shafa murnar samun kubuta daga hannun miyagun, ya kuma jaddada aniyar ‘yan sanda na ci gaba da kawar da miyagun laifuka a fadin jihar.
A wani labari kuma, Jami’an NIS Sun Cafke Bakin Haure da Suka Shigo Ba Bisa Ka’ida Ba Daga Kasashe Biyu
Hukumar kula da shige da fice ta Kasa reshen Jihar Ogun ta kama wasu mutane 33 da suka fito daga wurare biyu a karamar hukumar Odeda ta jihar.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Da yake holan wadanda ake zargin a ofishin ‘yan sanda da ke daura da fadar shugaban kasa a babban birnin jihar, Kwanturolan kula da shige da fice na jihar, Yakubu Jibrin ya ce wadanda ake zargin ba su da ingantattun takardun tafiya kuma ba su da wani izinin rayuwa.