By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an rundunar RRS sun dakile yunkurin wata mata da ba a tantance ba na kashe kanta a unguwar Iyana Oworo da ke jihar Legas.
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa matar da ta yi ikirarin cewa ana azabtar da ita a gida ta gudu ne domin ta kashe kanta a kan gadar Third Mainland Bridge.
Wani mahayi dake aike, daya ga matar tana tafiya cikin tuhuma a bakin Iyana Oworo na gadar, ya sanar da jami’an.
Wani sakon da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ya nuna cewa jami’an sun tsare ta bayan an sanar da su.
An ce an kai matar zuwa ofishin ‘yan sanda a yayin da ake kokarin jin ta bakin ‘yan uwanta.
Sanarwar ta kara da cewa, “Jami’an tawagar gaggawar da ke sintiri a gadar Third Mainland Bridge a yammacin yau, sun hana wata mata ki
kashe kanta ta hanyar tsalle ta fada cikin wani tafkin ruwa.
“Tana kokarin tsallawa cikin tafkin da ke wajen Iyana Oworo karshen gadar lokacin da jami’an suka tsare ta.
“Matar a cikin zantawar da aka yi ta bayyana cewa ‘An yi min duka a gida, shi ya sa na gudu dan na kashe kaina.
“Hankalin jami’an ya ja hankalin matar da wani mahayin da ya aike da su kafin su je wurin da lamarin ya faru don hana ta fadawa a cikin tafkin.