Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa sun kai samame a maboyar ‘yan ta’adda, inda suka kashe wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.
Rundunar, wacce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ta ce an gudanar da aikin ne a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba.
Karanta nanKotu Ta Daure Matashi Wata 4 A Kurkuku Saboda Satar Doya
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, Suleiman Nguroje, ya fitar, rundunar ta ce ta katse hanyoyin sadarwar masu aikata laifuka a sassan jihohin Taraba, Adamawa, Gombe, da Yobe da kuma Kamaru.
Jami’an rundunar ‘yan sandan da ke aiki da Crack Squad ne suka gudanar da shirin a wani aikin hadin gwiwa da mafarauta.
Sanarwar ta ce wadannan nasarorin sun biyo bayan dabarun hadin gwiwa da hukumar ta tsara don duba al’amuran da suka shafi garkuwa da mutane, fashi da makami, satar shanu, mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba, da dai sauransu.
PPRO ya bayyana cewa, jami’an ‘yan sanda da kuma mafarauta masu hadin gwiwa sun tsara wani aikintsaro a kusa da wasu maboyar da aka gano a ranar 30 ga watan Nuwamba.
A cewarsa, kokarin da aka yi ya samu nasara a ranar 3 ga watan Disamba, lokacin da wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne, suka ga mutanenmu anyi musayar wuta inda aka kashe biyu daga cikinsu, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
A wani labarin kumaFG ta amince da daukar likitoci 200 ga Asibitin Ogun
An samu nasarar kwato bindigu kirar AK-47 guda hudu da alburusai 92 daga hannun wadanda ake zargin.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, CP Afolabi Babatola, wanda ya yaba wa jami’ansa da mutanensa da kuma mafarauta da suke yi, ya umarce su da su bi wadanda suke gudu domin tabbatar da kama su tare da gurfanar da su gaban kuliya.