Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da satar gadaje makaranta 19 da katifa hudu a karamar hukumar Malam Madori da ke jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Lawan Shiisu, ya tabbatar wa manema labarai kamun a Dutse ranar Litinin.
Karanta nanHar Yanzu Akwai Wata Wuyar Kafin Jin Dadi A Nijeriya-Fasto Adeboye
A cewarsa, an kama wadanda ake zargin ne a ranar 27 ga watan Disamba bayan da ‘yan sanda suka samu labarin ayyukan wadanda ake zargin daga makarantar gwamnati Unity Senior Secondary School (GUSSS), Malam Madori.
Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin Muhammad Nadabo mai shekaru 40 da kuma Auwalu Muhammad mai shekaru 24.
PPRO ya kara da cewa wadanda ake zargin dukkansu mazauna garin Malam Madori ne da laifin hada baki, inda suka kutsa cikin makarantar da misalin karfe 1:30 na safe inda suka sace gadajen karfe na dalibai 19 da katifu hudu.
Ya kara da cewa an kwato kayayyakin da aka sace daga hannun wadanda ake zargi a lokacin da aka kama su.
Shiisu ya ce, ‘yan sandan sun kuma kama wasu mutane biyu a karamar hukumar Babura bisa laifin yin kutse da satar gero na Naira 16,000 da tsabar kudi 44,000.
A wani labarin kumaGwamnatin Jahar Filato Ta Ayyana Zaman Makokin Mako Daya A Jahar
Ya bayyana cewa, wadanda ake zargin, Abdullahi Mujitafa, mai shekaru 19 kuma mazaunin Kofar Gaba, da wani karamin yaro (an sakaya sunansa), an kama su ne da wani bangare na gero da kudi N500 kawai a hannunsu.
PPRO ya kara da cewa, da aka yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun ambaci Habiba Haladu, mai shekaru 55, daga Kofar Arewa Babura, a matsayin mai karbar kayansu na sata.
A cewarsa, ana ci gaba da kokarin kamo wanda ake zargi da karban, yayin da aka gurfanar da dukkan wadanda ake zargin a gaban kotu.