A ranar Alhamis ne aka gurfanar da wasu mutane biyu a gaban kotun majistare dake Akure kan wata yarinya ‘yar shekara 14 da ta bace.
Wadanda ake zargin, Omolola Adebayo, mace mai shekaru 32 da Oluwatimilehin Agunloko, namiji mai shekaru 17, ana zarginsu da hada baki wajen aikata laifin sace su kuma suka aikata wani laifi.
Karanta nanGwamanatin Jahar Katsina Ta Kashe Naira Biliyan 10 Akan Harkar Tsaro
Sufeto Simon Wada, dan sanda mai shigar da kara ya ce wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 28 ga watan Oktoba a Owo da ke karamar hukumar Owo ta jihar.
Ya bayyana cewa Agunloko shine saurayin yarinyar da ta bata yayin da ake kyautata zaton cewa ita ce yayi tarho da ita na karshe.
Wada ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 516 na kundin laifuka Cap 37, Vol. 1 Dokokin Jihar Ondo ta Najeriya 2006 da sashe na 3 na dokar hana garkuwa da mutane da sace sace ta jihar Ondo.
Sai dai wadanda ake tuhumar kowanne ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi,da yake yanke hukunci kan neman belinsu, Alkalin kotun, Mista Damilo.
Ya bayyana cewar ba za a bayar da belinsu a yanzu ba har sai zuwa lokacin da jam’am ‘yan sanda zasu kammala bincike akan batan yarinyar mai shekaru 14 a Duniya.
A wani labarin kumaKotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Nasarar Abdullahi Sule Na Jahar Nasarawa
Agunloko ya bukaci kotu da ta wanke shi daga wannan zargi da ake masa inda ya bayyana cewar babu wani batu na cewar shine mutum na karshe da ya kira budurwar tasa a waya kafin batanta.
Ita kuma wadda ake tuhumarta da hada baki wajen sace yarinyar ta bayyana cewar kawai an lakaba mata wannan laifi wanda bata san hawa ba balle sauka,ta kuma bayar da tabbacin duk binciken da za a yi ba za a sameta da wani laifi ba.