Dubun wani matashi da yake zuwa masallatai da alkawarin zai ruguje su ya mayar da su na zamani daga bisani ya arce da ƙofofi, tagogi da kuma kwanukan rufin masallatan ta cika.
An kama wannan matashi ne baya da ya je ƙauyen Kanoke cikin karamar hukumar Kiyawa ta Jahar Jigawa, da zummar zai gyara wani masallaci.
Bayan kuma al’ummar yankin sun amince da shi, ya cire ƙofofi, tagogi da kuma rufin masallacin ya arce da su.
Kakakin ƴan sandar Jahar Jigawa, DSP Lawal Adam yace sun kama wannan matashin kuma tuni sun gurfanar da shi a gaban kotu.
Tuni dai al’umma ke ci gaba da Togo Ala-tsine ha wannan mutumin, wanda yake abu kamar ba musulmi.
Shisu ya tabbatar da hakan ne a wani sakon murya da ya aikowa da jaridar Dimokuraɗiyya, a daren juya Laraba.