Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wasu mutane bakwai da ake zargin ‘yan fashi da makami ne a jihar, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Umar Mamman Sanda, ya ce a ranar 22 ga watan Agustan shekarar 2022, da misalin karfe 9 na dare, jami’an rundunar sun gudanar da binciken kwakwaf cewa a daidai wannan rana da misalin karfe 02:30, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba su kusan bakwai dauke da makamai a kauyen Bangaji ta karamar hukumar Alkaleri da nufin kaddamar da hare-hare tare da sace wasu mutanen kauyen.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu: Yanzu: Malamai Mata Na Cocin Katolika Sun Shaki Iskar Yanci
Sai dai ya ce, “Aikin hadin gwiwa tare da mafarautan yankin ne suka fantsama zuwa wurin, daga karshe dai an kashe yan ta’addan biyu daga cikin su su, yayin da sauran biyar suka tsere zuwa inda ba a san inda suke ba dauke raunuka daban-daban.
Ya kara da cewa ana kan kokarin damke sauran masu wadanda ake zargin yan fashin ne.
A halin da ake ciki, Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bukaci jami’an da su kara kaimi tare da cafke sauran wadanda ake zargin.
AWANI LABARIN KUMA: PSC Ta Dakatar Da Daukar Sabbin Jami’an ‘Yan Sanda Bayan Zanga-zangar IGP
Hukumar da ke kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC) ta dakatar da daukar sabbin jami’an ‘yan sandan Najeriya.
Hukumar ta yi hakan ne kasa da sa’o’i 24 da babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya fusata kan wani tallata daukar aiki