Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen kisan wani jami’in soji, Laftanar Musa a Enerhen, karamar hukumar Uvwie ta jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, ne ya shaidawa Jaridar DAILY POST cewa “an kama mutanen biyu.”
A cewarsa, “Ban ce su ne suka kashe jami’in sojan ba. Ba ni ne zan ce haka ba.”
Wakilin majiyar Jaridar Dimokuradiyya a baya ya ruwaito cewa marigayin, wanda shi ne Shugaban Ayyuka na Sojojin Najeriya, a sashin Bataliya ta 3 a Effurun, wasu ‘yan bindiga sun harbe shi ne a ranar Juma’a 11 ga watan Maris a kan hanyar Enerhen.
An bayyana cewa marigayin yana cikin motar sa ne a lokacin da ‘yan bindigar suka kama shi suka harbe shi har lahira.
Tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Sai dai lamarin ya haifar da tashin hankali a garin Effurun da kewaye yayin da jami’an tsaro suka fara farautar ‘yan bindigar.
Comments 1