Yan sanda a Taraba sun kama wani da ake zargin mai kera bam ne.
An kama wanda ake zargin ne a garin Tella da ke karamar hukumar Gassol a jihar, a yau Laraba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an gano na’urori daban-daban na kera bam a gidan wanda ake zargin wanda ake zargin ya yi amfani da gidan a matsayin masana’anta.
Hakazalika, an kuma yi zargin an kwato makamai da alburusai daban-daban daga hannun wanda ake zargin.
Wanda ake zargin, wanda aka ce dan jihar Zamfara ne, yana tsare a ofishin ‘yan sandan Taraba da ke Jalingo.
Jihar Taraba ta sami jerin hare-haren bama-bamai a watan da ya gabata.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba DSP Usman Abdullahi ya tabbatar da kama wanda ake zargin da kera bam amma bai yi karin bayani ba, kan lamarin.