By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne bayan sun kai hari tare da daba wa wani mazaunin unguwar Ja’in makami da ke cikin babban birnin jihar.
DUBA WANNAN LABARIN: Da Duni-duminsa: EFCC Ta Kama Tsohon Gwamna Willie Obiano A Filin Jirgin Saman Jihar Legas
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, daya daga cikin wadanda ake zargin, Mujahid Aminu mai shekaru 18, an kama shi ne bayan da wasu gungun jama’a suka samu nasara damke shi bayan sun far wa mazauna unguwar, yayin da ‘yan sanda suka kama dayan mai suna Sani Alkasim mai shekaru 18, shi ma a Unguwar ta Ja’in.
“Mun samu rahoton cewa wasu ‘yan fashi da makami guda biyu sun far wa wani mazaunin Unguwar Ja’in dake Kano, inda suka daba masa wuka a bangaren hagu na saman kirjin sa, sannan suka tafi da wayarsa ta Infinix S5 da kudinsa ya kai Naira 98,000, inda daya daga cikin wadanda ake zargin ya makale ne tare da kai farmaki.
“Nan da nan aka garzaya da wanda iftila’in ya afkawa zuwa asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano, inda aka kwantar da shi.
“An ceto wanda ake zargin da wasu gungun jama’a suka makale aka kuma garzaya da shi asibitin kwararru na Muhammad Abdullahi Wase Kano inda aka yi masa jinya kuma aka maida shi hannun jami’an ‘yan sanda,” in ji kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa.
Da suke amsa laifinsu, wadanda ake zargin sun ce: “Mun same shi a gidansa yana sanya katin waya , muka karbi wayar muka tafi, sannan muka dawo muka daba masa wuka a kirjinsa.
“Ya yi ihu kuma an kama daya daga cikin mu. Mun riga mun yi nadamar ayyukanmu kuma ba za mu sake yin hakan ba.”
Sai dai Kiyawa ya ce binciken da aka gudanar ya sa aka kama wani Murtala Sa’idu Sharif mai shekaru 34 a Unguwar Ja’in dake Kano, wanda yake kerawa tare da samar da makamai ga ‘yan fashi da makami.
“An kwato wukake guda uku. An mayar da shari’ar zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar domin yin bincike mai zurfi.”
Comments 1