By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wata fitacciyar ‘yar damfara mai suna Osasi Chinozom Juliet, mai shekaru 24, wadda ta kware wajen damfarar mutane a wuraren cirar kudi na ATM a cikin manyan biranen jihar.
DUBA WANNAN LABARIN: Hukumar DSS Ta Kama Wata Mata Mai Shayarwa Tare Da Masu Garkuwa Da Mutane A Jihar Ondo
Wanda ake zargin wanda aka kama tana dauke da katin cirar kudi na ATM na bankuna daban-daban har guda 17, ta amsa laifinta.
A cewarta, tana da katin cirar kudi na ATM na kusan dukkan bankunan dake fadin jihar Kano, wanda hakan ya sa ta samu sauki wajen musanyawa wadanda ta damfara na’urar katin cirar kudi na ATM, inda ta bayyana cewa ta ciro kudi daga asusun mutane da dama bayan ta musanya musu katin cirar kuti na ATM din.
Da yake tabbatar da kamun, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce wanda ake zargin tana cikin jerin sunayen wadanda ake nema ruwa a jallo, kuma an kama ta ne a lokacin da suke aikin sanya ido.
“Tawagar ‘Operation Puff Adder’ karkashin jagorancin SP Daniel Itse Amah, jami’in ‘yan sanda reshen Nassarawa, yayin da suke sintiri a kan hanyar Murtala Mohammed, sun tare Osasi Chinozom Juliet, dake kan titin Enugu, Sabon Gari Kano.
“Bayan kama ta, wani mai suna Yusuf Tijjani, ‘m’, ya koka da cewa, a ranar 17/03/2022, wanda ake zargin ya tuntube shi a lokacin da yake neman taimakon na’urar ATM, da yaudara, ya kuma canza masa katin ATM, sannan ya ciri kudi Naira 15,000:00 daga cikin asusunsa.
“Bincike cikin hankali ya nuna cewa wanda ake zargin ya yaudari tare da musanya katin ATM na mutane da yawa da abin ya shafa, ta kuma fitar da kudi daga asusun ajiya na bankinsu.
Sannan yace za’a gurfanar da ita a gaban kotu da zarar an kammala cikakken bincike kan lamarin,” in ji PPRO.