A ranar Laraba ne ‘yan sanda suka ceto wani dattijo mai shekaru 67 da aka kulle a daki sama da shekaru 20 a Kaduna.
Daily Trust ta ruwaito cewa, An gano mutumin ne tsirara kuma an kulle shi a wani daki a wani gida da ke hanyar Bayajidda a cikin garin Kaduna.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Ƙaramin Yaro yayi Garkuwa da Kansa don karɓar Miliyoyin Nairori daga Iyayen sa
Mazauna ginin sun gudu a lokacin da tawagar ‘yan sanda suka isa gidan.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewa za a gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Jalige ya ce wasu jami’an kiwon lafiya na muhalli ne suka fara gano mutumin mai suna Ibrahim Ado da ke gidan a bakin aiki.
“Sun kai rahoto ga sashin ‘yan sanda na Magajin Gari, kuma kwamishinan ‘yan sandan ya umurci jami’ai da su kwashe wanda abin ya shafa.
Ya kara da cewa “Ya kuma ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin don bankado al’amuran da suka shafi kulle mutumin da kuma dalilin da ya sa aka kebe mutumin na tsawon wannan lokaci,” in ji shi.
Jalige yace an kai mutumin asibiti domin a duba lafiyarsa.
(NAN)
A WANI LABARIN KUMA: Hatsarin Mota ta hallaka masu fasa Ƙwauri uku a Jigawa
Wasu mutane uku da ake zargin masu fasa kwauri ne sun mutu a wani hatsarin mota a karamar hukumar Babura da ke jihar Jigawa.
Wani mazaunin garin ya shaidawa DAILY POST cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da wata mota kirar Honda Accord 2006 ta rasa iko akan hanyar Babura zuwa Sule Tankarkar