Daga: Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta cafke wani gujajjen fursunan gidan yarin Kuje mai suna Kamala Lawal Abubakar.
An kama shi dauke da wani kunshi da ake zargin ganyen tabar wiwi ne.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/osun-dan-takarar-gwamna-na-prp-da-jamiyyar-sun-sami-sabani-saoi-24-kafin-zabe/
Kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, Gambo Isah, ya shaida wa manema labarai cewa, an kama fursunan ne bisa wasu sahihan bayanai.
Ya ce: “Jami’an ‘yan sanda na Danmusa da tawagar sun kai samame a maboyar ‘yan ta’adda a karamar hukumar Danmusa inda suka yi nasarar cafke wani mai suna Kamala Lawal Abubakar mai shekaru 33 a Unguwar Sale, dake karamar hukumar Danmusa.
“Abubakar wanda ake zargin ya gudu ne daga kurkukun Kuje, Abuja. A yayin gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya tsere daga gidan yarin Kuje dake Abuja, a lokacin da aka fasa gidan yarin”.
“An kuma gano wasu busasshen ganyen da ake zargin tabar wiwi na Indiya ne a hannunsa yayin binciken ‘yan sanda.”
“Za a mika wadanda ake zargin ga hukumar kula da gidan gyaran hali ta Najeriya, domin daukar matakin da ya dace”.
A wani labarin makamancin haka, rundunar ta kuma kama wasu gungun ‘yan fashi da makami da suka addabi yankin Katsina da kewaye.
Isah ya ce masu laifin da aka kama sun hada da: Abdulrazak Isyaku, mai shekaru 25, da Muhammad Abubakar mai shekaru 18, dukkansu ‘yan Kambarawa.
Ya ce: “Shahararrun ‘yan fashi ne, wadanda suka kware wajen kutsawa gidajen zama a Katsina da kuma yin fashi da makami da daddare.
“An kama wadanda ake zargin bisa ga sahihan bayanan sirri, a Kambarawa Katsina, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike an gano wasu babura guda biyu da aka sace na Motobi, kalar ruwan toka, mara rijista da Hijoe mai launin ja, mai lamba KTN 89 QN. .
“Wadanda ake zargin sun amsa laifin kai wasu hare-hare na fashi da makami a jihar, kuma sun ambaci wani Muhammed Lalo, wanda a halin yanzu yake hannunsu, a matsayin wanda ya taimaka musu.”