By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ceto mutane 24 da aka sace a kauyen Gurgurawa da ke karamar hukumar Bungudu a jihar.
Da yake jawabi ga manema labarai, mai magana da yawun rundunar, SP Mohammed Shehu, ya ce an kubutar da wadanda harin ya rutsa da su ne bayan wani artabu tsakanin jami’an tsaro da ‘yan fashin.
Ya ce, “A ranar 18 ga watan Fabrairun 2022 da misalin karfe 23:00 na safe, jami’an ‘yan sanda da ke aiki da rundunar ta 42 PMF Squadron Gusau, da ke yaki da ‘yan fashi da makami a yankin Gurgurawa a karamar hukumar Bungudu, sun samu kiran gaggawa cewa, ‘yan bindiga da dama sun mamaye kauyen Gurgurawa tare da sace wasu ’yan uwa.
“Lokacin da aka samu bayanan, masu aikin sashin basira tare da hadin gwiwar kungiyar ‘yan banga a yankin sun shiga cikin aiki tare da tattarawa zuwa wurin don aikin bincike da kuma ceto”.
“Lokacin da suka ga jami’an, ‘yan fashin sun ci su da wani mummunan yakin da ya dauki tsawon awa daya.”
Shehu ya ci gaba da cewa, sakamakon irin karfin wutar da jami’an tsaron suka yi, ‘yan bindigar sun gudu suka bar wadanda abin ya shafa a wurin.
Ya ce, ‘Yan sanda sun ceto wadanda lamarin ya rutsa dasu kimanin 24 kuma an duba lafiyarsu tare da tantance su bi da bi”.
Shehu ya kara da cewa, “Kwamishanan ‘yan sanda, CP Ayuba N. Elkana ya yabawa jajircewar da jami’an suka yi, ya kuma umarce su da su ci gaba da gudanar da aikin.
“Kwamishinan ya kuma baiwa ‘yan sanda tabbacin ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen kalubalen tsaro da ke addabar jihar”.