A ci gaba da nuna damuwa kan yadda ’yan bangar siyasa da aka fi sani da ‘Sara-Suka’ ke ci gaba da ta’addanci kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba wajen kuntatawa rayuwarsu.
Yanzu haka gwamnatin jihar Bauchi tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan jihar na shirin kafa kotun tafi da gidanka da za ta yi gaggawar gurfanar da ‘yan bangan siyasa a gaban kuliya bisa aikata laifuka daban-daban, Tribune Online ta rawaito.
KARANTA WANNAN: Gwamna Bago Zai Nada Mata 100 A Gwamnatinsa
Gwamnan jihar Sanata Bala Mohammed Abdulkadir ne ya bayyana hakan a lokacin da yake karbar bakucin sabon kwamishinan ‘yan sanda Musa Muhammad Auwal a gidan gwamnatin jihar Bauchi a ranar Talata.
Gwamnan ya bayyana cewa yana daya daga cikin kudirin magance yawaitar tashe-tashen hankulan da matasa ke haifarwa musamman matsalar yaran Sara Suka da ya fi kamari a cikin babban birnin jihar.
A cewarsa, gwamnatinsa za ta kuma bullo da shirye-shiryen karfafawa da nufin sanya matasan da ba su da aikin yi a cikin sana’o’i masu amfani domin kawar da su daga munanan dabi’u.
Bala Mohammed ya ce, “Muna matukar godiya da karbar bakonmu na watan Agusta. Muna kuma gode wa IGP wanda ya aiko da kwazo da juriya irinku idan aka yi la’akari da ci gaban ku.”
Sannan ya jaddada cewa, “A Bauchi, mun fahimci bukatar yin hadin gwiwa da Gwamnatin Tarayya don samun isassun ci gaba, sauye-sauye da kare lafiyar al’ummarmu wanda a cikinsa muka samu gagarumin taimako kuma muna sa ran samun hadin kai da ci gaba.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Kwamishinan ‘yan sandan ya ce a hankali ayyukan masu aikata laifuka na kara ta’azzara saboda haka an dauki kwararan matakai don tabbatar da tsaron ‘yan kasa.
Sabon kwamishinan ‘yan sandan da aka nada, Musa Muhammad Auwal, ya amince da kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta, ya kuma shaida wa Gwamnan cewa tuni aka fara daukar matakan ceto jihar daga munanan ayyukan.
A cewarsa, bayan hawansa mukamin, ya ziyarci tare da neman tallafi daga shugabannin gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro na ‘yan uwa a wani yunkuri na karfafa hadin gwiwa.
Kwamishinan ‘yan sandan ya ci gaba da cewa, “Na yi niyyar kirkirowa tare da fadada dukkanin ilimin da muke da shi na dakile miyagun ayyuka a jihar Bauchi duba da yadda na yi ta bincike da dama kan salon shugabancin Gwamna Bala daya yi.
“Nagano cewa shi shugaba ne mai son hada kai da bayar da duk wani abin da ya dace wajen ganin an samu zaman lafiya a Bauchi.”
A wani labarin kuma, Yadda Wata Ambaliyar Ruwa Ta Yi Awon Gaba da Direban Okada
A yammacin ranar Talata ne wani direban baburin Okada da ba a san ko wanene ba wata ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da shi.
Lamarin ya faru ne a yankin Chikakore da ke Kubwa, garin tauraron dan adam a karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja.