Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, a ranar Asabar ya ce ‘yan ta’addan da ke kashe Musulmi a jihohin Katsina, Borno, da Neja, su ne wadanda ke kashe kiristoci a Kudancin Kaduna, Benue, da Filato.
Sani ya ce ta’addanci ba shi da alaka da addini, inda ya kara da cewa suna bayan harin da aka kai musu ne kawai.
Karanta nanAbinda Yasa Na Cire Naira Miliyan 585 Daga Asusun Gwamnati Zuwa Asusuna-Beta Edu
A shafinsa na twitter Shehu Sani ya rubuta cewa yan ta’addan da ke kashe Musulmi a Katsina, Zamfara, Borno, Yobe da Niger, su ne ‘yan ta’addan da ke kashe Kiristoci a Kudancin Kaduna, Benue da Filato; ta’addanci ba shi da fifikon addini.
Babu wani addini da ya amince da tayar da zaune tsaye a Duniya,don haka duka mutane daya ne masu kisan Kiristoci da musulmin Nijeriya.
Hakan na zuwa ne bayan wasu ‘yan ta’adda sun kashe mazauna wasu al’ummomi a kananan hukumomi uku na jihar Filato a jajibirin Kirsimeti.
A wani labarin kumaYan Sanda A Jahar Yobe Sun Tsananta Bincike Akan Mutuwar Ammi Mamman
Wani matashi, mai suna Abubakar Musa, dan shekaru 43 da haihuwa dake zaune a gidajen Gwamnati da ake kira “Bra-Bra Housing Estate Damaturu”, ya shiga komar ‘yan Sanda a Jahar Yobe inda yanzu haka yake fuskatar bincike kan kisan gilla da akayi wa Matar sa Ammi Mamman mai shekaru 42 da haihuwa ranar Alhamis da ta gabata.
Sanarwa mai dauke da sa hannun Jami’in hulda da Jama’a na Hukumar ‘Yan Sandan Jahar, DSP Dungus Abdul-Karim, tayi nuni da cewa, hukumar ta samu kiran gaggawa a ofishin ta sashe na uku (C Division) da misalin karfe 4:48 na asubahi ranar Alhamis 4 ga watan Janairun shekara ta 2024 inda aka baiwa hukumar labarin kisa a unguwar Bra-Bra dake kan hanyar da ta kewaye birnin Damaturu tsakanin hanyar Maiduguri da Gujba.
A cewar sanarwar, an kashe matar aure mai suna Ammi Mamman yayin da take kwance da mijin ta Abubakar Musa ta hanyar yanke mata wuya wanda yayi sanadin mutuwar ta.