Janar Lucky Irabor, Babban Hafsan hafsoshin Tsaron kasar nan (CDS), ya bayyana cewa akalla ‘yan ta’addar Boko Haram 51,828 da iyalansu ne suka mika wuya ga gwamnatin tarayyar Najeriya tsakanin Yuli 2021 zuwa Mayu 2022. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Irabor ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da lacca mai taken “Manufar Tsaro ta Kasa da Tsarin Adalci na Gaggawa a Yaki da Ta’addanci a Najeriya” a bikin ranar kafa Jami’ar Jihar Edo karo na 7, dake garin Uzairue, a karamar hukumar Etsako ta Yamma ranar Asabar.
KU KARANTA: FG Ta Kammala Ayyukan Lantarki 1,375 A Yankunan Karkara
CDS ya kuma ce, tubabbun ‘yan ta’addan Boko Haram 1,543 ne suka yaye a sansanin Mallam Sidi da ke Gombe tsakanin shekarar 2016 zuwa 2022.
Irabor ya ce, “Tsakanin Yuli 2021 zuwa Mayu 2022 kadai, a kalla ‘yan Boko Haram 51,828 da iyalansu ne suka mika wuya, daga cikinsu 13,360 mayakan ne.”
“Shirin (wanda aka fi sani da Operation Safe Corridor) yana ba da damammaki masu yawa, kuma an tsara wa wadanda suka tuba shirin ne don horar da su sana’o’i domin sauya tunanin su wjaan komawa cikin al’umma,” in ji shi.
A halin da ake ciki, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kwashe shekaru takwas tana yaki da kungiyar Boko Haram.
Rahotanni sun nuna cewa, Gwamnatin Buhari ta samu gagarumar nasara a kan ‘yan ta’adda, saboda da dama sun mika wuya ga gwamnati.
A wani labarin kuma, Yan Adawa Na Shirye-Shiryen Dakatar Da Rantsar Da Tinubu – Keyamo
Daraktan hulda da jama’a na zababben shugaban kasa kuma karamin ministan kwadago Festus Keyamo (SAN) ya yi fatali da shirin da jam’iyyun adawa suka yi na dakatar da bikin rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu. Kamar yadda Daily Trust ta ruwairo.
Keyamo, wanda ya bayyana hakan a ranar Asabar a wata sanarwa mai taken ‘Sanarwa Kan Shirye-Shiryen Zanga-zangar adawa da Jam’iyyun adawa: Shiru su, Ba Matsorata ba’, ya ce wadannan mutane sun yi kira da “ko dai a soke sakamakon zaben ko kuma kada a rantsar da zababben Shugaban kasa a ranar 29 ga Mayu, 2023.