Al’ummar Tunisiya na kada kuri’a a zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin kasar mai cike da cece-kuce wanda zai bai wa shugaban kasar Kais Saied wasu manyan mukamai da ya kwace.
Idanba’a manta ba, a shekarar da ta gabata ne dai Kais Saied ya rushe majalissar dokokin kasar.
Sabon kudirin kundun tsarin mulkin zai bai wa shugaban cikakken iko yayin da yan majalissun za su kasance karkashinsa tare da cire wasu shamaki na karfin ikonsa.
Mista Saied da magoya bayansa sun ce ana bukatar sauye-sauyen domin kawo karshen bangaranci na siyasa da cin hanci da rashawa da ya dabaibaye Tunusiya.
Sai dai masu suka sun ce sauye-sauyen za su kawo karshen tsarin dimokuradiyyar da aka taba yi bayan boren jama’a a shekara ta 2011 wanda ya yi sanadiyar hambarar da tsohon shugaban kasar mai ci, Zine al-Abidine Ben Ali daga mulki.
A wani labari kuma na daban.
Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ma’aurata a Abuja
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wasu ma’aurata biyu a kauyen Sheda da ke karamar hukumar Kwali a Abuja.
Wani dan uwan ma’auratan da ke zaune a Goni Gora Kaduna, Alih Moses ya shaidawa Jaridar DAILY POST, a ranar Litinin, cewa an yi garkuwa da kaninsa, Mista Sunday Odoma Ojarume da matarsa Mrs Janet Odoma Ojarume daga gidansu da safiyar Lahadi, yayin da ‘yan bindigar suka shiga gidansu. al’umma da manyan makamai, suna harbi lokaci-lokaci.
Ya ce masu garkuwa da mutanen sun ajiye kansu ne a wurare masu mahimmanci a cikin yankin.
A cewarsa, al’ummar kauyen Sheda sun kasance cikin tashin hankali a ranar Lahadin da ta gabata, saboda harbe-harbe da masu garkuwa da mutane suka yi a wasu wurare masu muhimmanci, kafin su yi garkuwa da ma’auratan.
Ya ce shugaban ‘yan bindigar ya saki matar ne a lokacin da ake kai su dajin, inda ya bukaci ta je ta nemi kudin fansa.
DSP Adeh Josephine, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, bai amsa kiran wayar da akayi masa ba domin tabbatar da harin.