Malaman addinin Islama sun ce masu magudin zabe da masu damfara ta yanar gizo da aka fi sani da Yahoo boys na azumi a banza, sai dai idan sun tuba baya. Kamar yadda Punch ta ruwaito.
Babban Limamin Jami’ar Abuja, Farfesa Taofik Azeez, da Kungiyar Matasan Musulunci ta Mishan, Abeokuta, Ustadh Jubril Awwal, ne suka bayyana haka a ranar Laraba yayin da suke zantawa da wakilin majiyar Dimokuradiyya a Abeokuta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Fani-Kayode ya yi wani tsokaci, bayan DSS ta bankaɗo shirin kafa gwamnatin wucin gadi
Babban limamin Abuja, wanda kuma shi ne babban mai wa’azi na Dawah Front na Nigeira, ya ce Yahoo Boys na bata lokacinsu da azumi ne kawai sai dai sun tuba.
Malamin ya ce ko da masu damfara ta yanar giO sun yi amfani da kudaden haramtatun ayyukansu wajan ginin masallaci, ba za a su sami ladan shi ba.
Ya ce: “Zunubi ne. Suna sace kudin mutane ta hanyar yaudara. Ko da sun kashe kudinsu wajen gina masallatai Allah ba zai karba ba, domin Allah mai tsarki ne, ba ya karbar komai sai mai tsarki.
“Yan Yahoo, masu garkuwa da mutane suna azumin banza ne. Dole ne su tuba, kuma su guji komawa kan ayyukan su bayan Ramadan.”
Mishan na IYL, a nasa jawabin, ya ce masu magudin zabe da Yan Yahoo masu azumi suna azumi a banza.
Ya ce: “Watan Ramadan shi ne watan da ake kara samun kusanci da Allah. Ma’anar Ramadan shine tsoron Allah.
“Idan wani ya yi fasikanci, babu yadda za a yi a karbi azuminsa face ya tuba.”
Shi ma da yake nasa jawabin, Limamin Masallacin ‘Yanci da ke Abeokuta, Ustadh Rasheed Adeyanju, ya gargadi masu magudin zabe da Yan Yahoo da su guji shan kishin ruwan banza.
A wani laabrin kuma, Hisbah Ta Lalata Kwalaben Giya Sama Da Milliyan Biyu
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta lalata fiye da kwalaben barasa miliyan biyu da aka kwace a jihar. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Hukumar ta ce matakin wani mataki ne na karfafa yaki da shigo da barasa da kuma sayar da barasa, wanda haramun ne a jihar.