Yanzu Jaruman Fim sun fi fina-finan yawa — In ji Suwaiba Abubakar
Duk wata Jaruma da take cikin harkar fim da wadda ta daɗe da kuma sabuwar shigowa idan kun yi magana da ita babu abin da za ta ce sai burin ta yi aure.
Ita ma Jaruma Suwaiba Abubakar Makauniya haka ne burin na ta kamar yadda ta bayyana wa wakilin mu a lokacin tattaunawar da muka yi da ita in da ta fara da cewa “Ni ba sabuwar Jaruma ba ce a wannan masana’anta ta Kannywood, domin ina ganin zan kai shekaru 15 zuwa 16 don haka na ga abubuwa a cikin ta.
“Domin idan ka duba a baya harkar tana da tsari sosai, saboda a wancan lokacin muna da tsarin Ubangida wanda idan Mutum zai yi aiki, to ba zai yi aiki da ke ba sai ta hanyar Ubangidan ki, wannan ya sa a wancan lokacin duk mun san kan mu”
Ta ƙara dacewa “Amma a yanzu kana ma tafiya a kan hanya sai ka ga yarinya ta ce ita ‘yar fim ce ka rasa ma wanne fim ta yi, sai ta yi maka dogon bayani ka kasa gane ta saboda finafinan ba irin na da bane da kowa zai saya ya kalla, don yanzu duk finafinai sun koma YouTube channel kuma ba kowa yake kallo ba.
Haka zalika su masu kallon ba su ma damu da sai sun ga Jaruman ba, saboda a yanzu Jaruman sun fi fina-finan yawa don haka da yarinya ta zo an dan fara haska ta ana ganin ta a YouTube, sai ta rinka daukar kanta ita ma Babbar Jaruma ce.
Acewar ta “saboda haka idan ma kuka gamu taki gaishe ka, duk da kin riga ta shiga harkar fim kuma kin fi ta a shekaru.”
“Don haka a yanzu duk da ina yin aikin ba wai na daina bane, saboda ni a yanzu na girma ina dai bin abin a hankali, don haka a yanzu na fi mayar da hankali na a kan harkar wakokin siyasa da na gidan biki. Saboda haka a yanzu ni abin da na tsara wa rayuwa ta ta gaba, shi ne fatan samun miji nagari da zai aure ni mu zauna zaman aure cikin kwanciyar hankali”.
“Don haka babban burina in samu Miji nagari da zai zama Mijina kuma Uban ‘ya’yana, kullum addu’a ta, Allah ya cika mini burinan nawa.”
A wani labarin kuma: Zaɓen 2023: CBN ya musanta shirin rufe wasu ayyukan Banki
Babban bankin Najeriya (CBN) ya musanta shirin rufe ayyukan banki gabanin zaben shugaban kasa da za a yi a ranar Asabar.
Rahotanni sun bayyana cewa za a rufe ayyukan banki daga ranar Alhamis, 23 ga Fabrairu zuwa Litinin, 27 ga Fabrairu, 2023.