- Abubakar Suleiman ya sake zama shugaban majalisar dokokin jihar Bauchi
- An zabi Suleiman a natsayin kakakin majalisar dokokin Bauchi ba tare da wata hamayya ba
- Dukkansu an zabe su ne a wajen kaddamar da majalisar ta 10
An sake zabar Abubakar Suleiman a matsayin shugaban majalisar dokokin jihar Bauchi,Punch ta rawaito.
A ranar Talata ne aka sake zabensa ba tare da wata hamayya ba.
KARANTA WANNAN: PTDF ta fitar da sunayen ‘Yan Najeriya Dubu 5000 don basu tallafin karatun kasashen waje
Suleiman wanda ya kasance yana wakiltar mazabar Ningi ta tsakiya.
Haka kuma an zabi Jamilu Barade, mamba mai wakiltar birnin Bauchi a matsayin mataimakin kakakin majalisar.
Dukkansu an zabe su ne a wajen kaddamar da majalisar ta 10 da ke gudana yanzu haka a harabar majalisar da ke Bauchi.
A wani labarin kuma,Tsohon Minista Ya Maida Martani Kan Matakin Tinubu Na Korar Hafsoshin Tsaro
Tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigo a jam’iyyar APC, Femi Fani-Kayode, ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu kan ficewar da ya yi a siyasance cikin makonni uku da suka gabata.
A halin yanzu dai ana yaba wa shugaban kasa kan gyare-gyaren da ake yi da kuma tsaftace tsarin, wanda ya fito fili ta hanyar cire wasu manyan mukamai.
Tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, Tinubu ya kori tare da maye gurbin wasu jami’an gwamnati.
A makon da ya gabata ne shugaban ya tsige gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emfiele. Bayan ‘yan kwanaki kuma an tsige Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa.