Mazauna rukunin gidaje 1000 a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun farka da fashewar wani abu da safiyar Asabar.
Fashewar da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka yi sanadiyar shi, ya kawo tashin hankali a tsakanin al’umar yankin.
Har ila yau wani makamin roka ya sauka a filin jirgin na Gomari, yanki mai tazarar kilomita hudu daga filin jirgin da ke babban birnin jihar.
A cikin wani faifan bidiyo da Jaridar Daily Trust gani, ta kuma ruwaito cewa, mazauna yankin na tattaunawa kan lamarin, a rukuni-rukuni.
An kuma ga dimbin jama’a a daya daga cikin gidajen da fashewar ta shafa.
Wani mazaunin garin ya ce ba a samu asarar rai ba a lamarin amma majiyar Jaridar Dimokuradiyya ba ta iya tabbatar da hakan da kanta ba, har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Wata majiyar soji ta bayyana cewa, dakarun da ke dauke da Bataliyar ta 33, a Njimtelo, sun bude wuta ne a lokacin da suka hango masu tada kayar baya a wajen birnin Maiduguri.
An kuma ce maharan sun kuma yi artabu da sojoji yayin harin.