Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya je gidan gwamnati domin ziyartar Shugaba Bola Tinubu bayan rantsar da shi a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa ta 10,Daily Post ta rawaito.
Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, ya doke abokin hamayyarsa Sanata Abdul’aziz Yari da kuri’u 63 inda ya zama shugaban majalisar dattawa.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Godswill Akpabio Ya Zama Sabon Shugaban Majalisar Dattawa
Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC na kasa ya amince da Akpabio a matsayin wanda ya fi son zama shugaban majalisar dattawa.
Sakamakon haka, wasu ’yan takara biyu, Orji Uzor-Kalu (APC Abia kuma tsohon gwamna da Osita Izunaso (APC Imo), sun fice daga takarar sakamakon lallashin jam’iyyar da shugaban kasa suka yi.
A wani labarin kuma,Da Dumi-Dumi: Kalu Ya Zama Sabon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai
Benjamin Kalu ya zama sabon mataimakin kakakin majalisar wakilai ba tare da wata hamayya ba
Kalu shi ne dan takarar da APC ta amince da shi a matsayin wanda zai zama mataimakin shugaban majalisar wakilai
Magatakardan majalisar shine wanda ya ayyana Kalu a matsayin mataimakin shugaban majalisar
Tuni dai tsohon kakakin kwamitin yada labarai da hulda da jama’a na majalisar, Benjamin Kalu ya zama mataimakin kakakin majalisar wakilai ba tare da wata hamayya ba.
Babajimi Benson daga jihar Legas ne ya tsayar da Kalu a matsayin wanda zai zama mataimakin shugaban majalisar wakilai sai kuma Khadijat Bukar Abba Ibrahim daga jihar Yobe ta tsaya takara.
Kalu shi ne dan takarar da APC ta amince da shi a matsayin wanda zai zama mataimakin shugaban majalisar wakilai.
Benson ya ce nadin ya zama tilas ne domin a hada shi da kuma magance wariya da ake gani.
Bayan kiran da a kara zaburar da shi ba tare da mai zuwa ba, magatakardan majalisar ya ayyana Kalu a matsayin mataimakin shugaban majalisar kuma ya ci gaba da gudanar da harkokinsa.