Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya isa Abuja daga birnin Landan na kasar Birtaniya, inda ya yi jinyar hakora a makon da ya gabata.
Jirgin Gulfstream ne ya kai Buhari bangaren shugaban kasa na filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu Yayi Ganawar Sirri Da Kwankwaso A Faransa
A ranar 30 ga watan Afrilu, jaridar PUNCH ta bayar da rahoton cewa an kai jirgin saman NAF 001 na Shugaban kasar zuwa wurin gyara dake Amurka, don ziyarar kulawa.
A cikin makonni biyun da suka gabata, an sake jigilar shugaban na Najeriya a wani jirgin saman shugaban kasa ciki har da ziyarar da ya yi a ranar 3 ga watan Mayu, inda ya bi sahun sauran shugabannin duniya a Landan don bikin nadin sarautar Sarki Charles III da Sarauniya Camilla.
Duk da cewa an shirya tafiyar za a yi kwanaki biyar, fadar shugaban kasar ta bayyana cewa an kara wa Buhari tsawon mako guda domin jinyar hakora.
“Zai ci gaba da zama a birnin Landan na kasar Birtaniya na tsawon mako guda, bisa shawarar likitan hakora da ya fara zuwa wurinsa,” wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya sanya wa hannu, ta bayyana a makare ranar Talata, 9 ga watan Mayu.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa ya zuwa yanzu Shugaba Buhari ya kwashe akalla kwanaki 232 yana balaguron lafiya tun bayan hawansa ofis a shekarar 2015.
A ranar 5 ga watan Fabrairun shekarar 2016, watanni takwas bayan hawansa mulki, shugaban ya fara ziyarar jinya ta farko zuwa birnin Landan na kasar Birtaniya, inda ya shafe kwanaki shida tsakanin ranar 5 zuwa 10 ga watan Fabrairu.
Ziyarar jinya ta biyu da Buhari ya yi ta biyo bayan wata hudu ne a ranar 6 ga watan Yunin shekarar 2016, inda ya shafe kwanaki 10 yana jinyar wani ciwon kunne da ba a bayyana ba bayan ya huta na karin kwanaki uku kafin ya dawo ranar 19 ga watan Yunin shekarar 2016.
A ranar 19 ga watan Janairun shekarar 2017, shugaban ya tafi ziyarar jinya mafi tsawo na biyu. Ya koma Abuja ne a ranar 10 ga watan Maris din shekarar 2017, inda ya shafe kwanaki 50 a can.
A watan Mayu wannan shekarar ne shugaban ya tafi birnin Landan domin gudanar da jinya mafi tsawo da ya shafe kwanaki 104.
Shugaban ba zai ziyarci Landan ba don sake duba lafiyarsa har sai bayan shekara guda a watan Mayu 2018 lokacin da ya kwashe kwanaki hudu kan “bita na likita.”
A karshen watan Maris din shekarar 2021, Buhari ya sake komawa Landan don duba lafiyarsa na yau da kullun, wanda ya dauki kwanaki 15.
Tafiyar tasa ta zo ne a daidai lokacin da ake fama da matsalar ma’aikata a fannin kiwon lafiya, lamarin da ya sa mambobin kungiyar likitocin Najeriya suka fara yajin aikin sai baba-ta-gani saboda rashin biyansu alawus-alawus.
A ranar 6 ga watan Maris din shekarar 2022, Shugaban ya tashi zuwa Landan don ziyarar jinya ta mako biyu wadda ta dauki tsawon kwanaki 12.
Tun da farko dai an shirya Buhari ya kai ziyara birnin Landan daga birnin Nairobi na kasar Kenya inda ya halarci taron Majalisar Dinkin Duniya kan kula da muhalli na shekaru 50.
Sai dai ya dawo Najeriya a ranar Juma’a 4 ga watan Maris, amma ya tafi Landan ranar Lahadi 6 ga watan Maris.
Tun da farko, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Femi Adesina, ya sanar da cewa Buhari zai wuce Landan daga Kenya don duba lafiyarsa na yau da kullun wanda zai dauki akalla makonni biyu.
A ranar 31 ga watan Oktobar shekarar 2022, shugaban ya tashi daga Owerri, babban birnin jihar Imo zuwa Landan domin wata duba lafiyarsa na tsawon makonni biyu. Ya komo kasar ne a ranar 13 ga watan Nuwambar shekarar 2022.
Mai magana da yawun shugaban ya kare tafiye-tafiyen da Buhari ya yi a kasar waje yana mai cewa “ya shafe shekaru 40 yana amfani da likitoci iri daya.”
Adesina ya kuma bayar da hujjar cewa yana da kyau Shugaban kasa ya tsaya tare da tawagar da ke da tarihin lafiyarsa.
A wani labarin kuma, Kwana Ya Kare: Yan Jarida Biyu A Najeriya Sun Kwanta Dama
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Oyo ta rasa mambobinta guda biyu.
Mambobin biyu sun mutu a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, kamar yadda jaridar DAILY POST ta ruwaito.