Ana fargabar sake shuga wani sabon yajin aikin jami’o’in gwamnatin Najeriya, yayin da kungiyar malaman jami’o’i, ta kasa wato ASUU, ke gudanar da taron majalisar zartarwarta (NEC) a birnin Calabar na jihar Cross River. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Majiyar Dimokiradiyya ta samu labarin cewa an fara taron ne a jiya, Asabar 3 ga watan Disamban shekarar nan da muke ciki, kuma har yanzu ana ci gaba da gudanar da wannan taro.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kungiyar Yan Jaridu NUJ Ta Karrama Sanata Uba Sani Da Lambar Yabo Ta Jin Kai
Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU dai ta fuskanci takaddamar ma’aikata da gwamnatin Najeriya kan rashin cika alkawuran da ta dauka da kuma ci gaba da kin biyan mambobinta albashin watanni takwas da kungiyar ta kwashe ta na yajin aiki.
Idan za a iya tunawa cewa, kungiyar ta janye yajin aikin watanni 8 a ranar 14 ga Oktoban shekarar 2022, bayan da shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya shiga tsakanin su da gwamnatin tarayya.
Sai dai gwamnati ta dage kan aiwatar da manufar ‘Ba Aiki, Ba Albashi’ na tsawon lokacin da ma’aikatan jami’o’in ba su yi aiki ba.
Wani mamba a kungiyar ta ASUU da ya zanta da DAILY POST daga Calabar, babban birnin jihar Cross Rivers, ya tabbatar da cewa kungiyar na taro a halin yanzu.
“Eh, muna yin taro, kuma taron yana ci gaba da gudana
Yanzu babu wata matsa da muka cimma wa domin ba a yanke hukunci na karshe ba.
“Batun shine muna daukar rahotanni ne kawai; a yanzu ba mu kai ga batun biyan albashi ba,” inji shi.
A halin da ake ciki, ASUU a makon da ya gabata ta umarci mambobinta da su yi zanga-zanga kan batun hana su albashi na watanni takwas.
Majiyar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa mambobin kungiyar ASUU na Jami’ar Legas (UNILAG), Jami’ar Nijeriya dake Nsukka (UNN), da Jami’ar Ibadan (UI), da dai sauransu, sun shiga zanga-zangar ne domin samun biyan bukatunsu.
A wani labari kuma, Ba Za Mu Bar Wani Ya RikiTa Najeriya ba — DSS
A jiya ne hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gargadi malaman addini na Musulunci da na Kirista da su daina tunzura ‘yan Najeriya kan gwamnati mai ci a kasar nan.
Rundunar tsaron ta farin kaya ta kuma gargadi shugabannin siyasa da su daina amfani da ‘yan daba wajen gudanar da ayyukansu, inda ta bukaci matasa da kada su mayar da kansu tamkar kayan aikin ‘yan siyasa.
Babban daraktan hukumar ta DSS, Yusuf Bichi ne ya yi wannan gargadin a Abuja a yayin bikin yaye daliban jami’ar leken asiri ta hukumar leken asiri ta 15 a cibiyar nazarin harkokin tsaro ta kasa.
Bichi ya ce musamman masu yin kalaman batanci a kan Najeriya ta yanar gizo da kuma ta wata hanya ta daban, ya kamata a yi la’akari da cewa, kasar nan ba ta cikakkiyan zaman lafiya ta fuskar tsaro.