Gwamna Masari na Jihar Katsina ya nuna rashin goyon bayansa game da shirin neman afuwa da Sheikh Ahmad Gumi yake so gwamnatoci su yi wa ‘yan fashin daji.
Masari ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da Channels TV da yammacin Laraba, inda ya nuna cewa “babu abin da malamin addinin ya sani” game da yunƙurin gwamnonin yankin a yaƙi da ‘yan fashin.
Masari ya ci gaba da cewa; “yana wurin ne? Me ya sani game da abin da muka yi a Kaduna? Na ƙalubalanci Gumi ya fito ya faɗa mana abin da ya san mun aiwatar a Kaduna,” a cewar Masari, yayin da yake martani game da ra’ayin Gumi kan salon gwamnoni a yaƙi da ɓarayin.
Yayin zagayen da Ahmad Gumi yake yi a cikin daji domin yi wa ‘yan fashin wa’azi, malamin ya ce mutanen sun faɗa masa cewa jami’an tsaro sun kashe musu ‘yan uwa da ƙwace musu dukiyoyi, abin da ya sa suka ɗauki makamai kenan.
Masari ya ce: “Abubuwan da suke faɗa masa (Gumi) a yanzu tun 2015 suke faɗa, shi suka faɗa a 2019. Me ya sani game da dazuka? Ko dai yana tausaya wa miyagu ne?”
Kazalika, gwamnan ya ce ba ya goyon bayan yunƙurin da malamin yake yi na shiga tsakanin gwamnoni da kuma masu aikata kashe-kashen da sace mutane domin neman kuɗin fansa.
Masari ya ce abin da ‘yan bindigar ke buƙata shi ne wa’azi da gyaran tarbiyya domin su gane munin abin da suke aikatawa na kashe-kashen mutane.
Kawo yanzu, kusan ɗalibai 800 aka sace tun watan Disamba a jihohin Kaduna da Zamfara da Neja da Katsina daga makarantunsu.