Yanzu-Yanzu: Gwamnan Katsina Ya Kori Wasu Jiga-Jigan Gwamnatin A Guda 4
Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya kori wasu manyan kusoshin Gwamnatin sa guda hudu.
Wannan na zuwa ne kwanaki biyu da gudanar da Babban zaɓen Najeriya na Shugaban Ƙasa da ƴan majalisu.
Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Alhaji Muntari Lawal ya sanyawa hannu aka rarraba wa Manema Labarai.
Sanarwar tace “A cikin yunƙurin ɗaukar madaidaicin dabarun sake daidaitawa da
gyara, Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina
Aminu Bello Masari, CFR, ya amince da dakatar da mutane a gwamnatin sa kamar haka;
Kwamishinan Ayyuka da Gidaje Hon, Tasi u Dahiru Dandagoro
Yust Barmo, Shugaban jihar Katsina
Hukumar Jin Dadin Alhazai,
Fatima Ahmad Sakatariyar Hukumar Kula da cimma muradun ƙarni.
Aminu Waziri
Sakatare na dindindin
Ma’aikatar Aikin Gona da
Albarkatun Kasa
An umurci duk waɗanda abin ya shafa dasu
mika mulki da
duk kadarorin Gwamnati da ke hannun su
Manyan Sakatarorin Dindindin ko Manyan Daraktoci .