- Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde , ya rattaba hannu kan gyaran dokar sarakunan Gargajiya.
- Makinde yana neman bai wa gwamna samun ikon cin gashin kansa don gabatar da nadin rawani ga sarakunan gargajiya a jihar.
- Gwamnan yace “Kafin shigowata majalisar sarakunan gargajiya ba ta aiki, amma yanzu tana iya aiki.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a ranar Juma’a, ya rattaba hannu kan gyaran dokar sarakunan gargajiya a jihar, Cap.28.
Makinde yana neman bai wa gwamna samun ikon cin gashin kansa don gabatar da nadin rawani ga sarakunan gargajiya a jihar.
KARANTA WANNAN: An Dage Sauraren Shari’ar Rarara Da Ake Zarginsa Da Taurin Bashi
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, majalisar dokokin jihar ta zartar da kudirin a zamanta na ranar Laraba, domin yiwa dokar sarakunan jihar Oyo ta shekarar 2000 kwaskwarima, Cap 28, bayan gabatar da rahoton kwamitin majalisar kan batun kananan hukumomi da Jiha.
Idan dai ba a manta ba,JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa a ranar Juma’a 12 ga watan Mayun 2023 ne majalisar dokokin jihar ta gudanar da taron jin ra’ayin jama’a kan batun gyaran da za’a yi, inda aka tattara ra’ayoyin masu ruwa da tsaki ciki har da sarakunan gargajiya.
Makinde, yayin da ya ke rattaba hannu kan gyaran dokar a zauren majalisar zartarwa da ke birnin Ibadan, ya yaba wa ‘yan majalisar kan yadda suka amince da ita a kan lokaci, domin hakan zai taimaka wa majalisar sarakunan gargajiya ta yi aiki mai kyau da kuma dakile kararrakin da ake tafkawa akai-akai.
Ya ce, “To, abin da ake nufi shi ne, dole ne a samar da wata doka a jihar da za ta ba da damar gudanar da harkokin majalisar sarakunan gargajiya lami lafiya, wanda ke da muhimmanci.
Gwamnan yace “Kafin shigowata majalisar sarakunan gargajiya ba ta aiki, amma yanzu suna iya aiki.
“Kun tuna cewa gwamnatin da ta gabata ta yi kokarin gyara tsarin majalisar sarakunan gargajiya, musamman a Ibadan.
“Gwamnati ta ba wa wasu manyan hakimai damar nada rawani ga kananan sarakuna.
“Daya daga cikin manyan Hakimai ya je kotu, kuma kotun jihar ta yanke hukuncin cewa gwamnatin da ta shude ba ta bi nasu dokar ba.
“Yanzu da muka gyara dokar, za mu bi namu, kuma babu wanda zai iya zuwa kotu a yanzu ya yi nasara.”
Tun da farko mataimakin shugaban majalisar jihar Mohammed Fadeyi, yayin da yake gabatar da kudurin dokar ga gwamnan, ya ce an yi taron jin ra’ayin jama’a kan dokar da aka yi wa kwaskwarima a majalisar inda aka tattara ra’ayoyin masu ruwa da tsaki ciki har da sarakunan gargajiya.
Fadeyi ya ce sabuwar dokar za ta yi tasiri sosai a jihar.
Olubadan na Ibadan Oba Lekan Balogun, wanda ya samu wakilcin Balogun, Olubadan na Ibadan, Chief Owolabi Olakulehin, ya jagoranci Olubadan-in-Council da sauran sarakunan gargajiya wajen bikin.
A wani labarin kuma,Yan Najeriya Da Kansu Zasu Roƙi Tinubu Domin Wa’adi Na Biyu – Betta
Shugabar mata ta jam’iyyar APC ta kasa, Betta Edu, ta ce zababben shugaban kasa, Bola Tinubu zai taka rawar gani ta yadda ‘yan Najeriya za su roke shi ya sake tsayawa takara a karo na biyu.
Tinubu ya ce za a rantsar da shi a matsayin babban shugaban Tarayyar Najeriya a ranar 29 ga Mayu, 2023.