Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tarayya ta fitar da sunaye da hotunan Ƴan Ta’addan da suka tsere daga Yarin Kuje
Gwamnatin Tarayya ta fitar da sunayen ƴan ta’addan da suka tsere daga Gidan Yarin Kuje, a lokacin da Mayaƙan Ƙungiyar Ta’addanci ta ISWAP ta shiga wurin.
Daily Trust ta ruwaito yadda Ƴan Ta’addan suka kai hari a gidan yarin Kuje dake Babban Birnin Tarayya Abuja a daren ranar Talata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwamitin Uba Sani a Majalisar Dattijai ya tantance Umar Yahaya a matsayin Shugaban Hukumar UFTF
Bashir Magashi, Ministan Tsaro, yace dukkanin ƴan ta’addan dake tsare, ƴan Ta’addan sun sake su.
A ranar Juma’a, Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Aƙidu na Ƙasa (NCoS) ta saki sunaye da hotunan wasu daga cikin wanda suka tsere.
Daga cikin ƴan ta’addan da aka saki hotunan su, da sunayen su, sun ƙunshi Abdulkareem Musa, da Abdulkareem Adamu, da Abubakar Abibu, sa Kuma Abubakar Yusuf.