By Abbas Yakubu Yaura
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon gwamnan Imo Sanata Rochas Okorocha a hannun hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC har sai an yanke shawarar neman belinsa.
Okorocha wanda yanzu haka yake a hannun EFCC, jigo ne a jam’iyyar APC, kuma aminin tsohon gwamna, Anyim Nyerere Chinenye.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-dumi: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Rediyo A Anambra, Sun Kona Motoci Da Gini
Mai shari’a Inyang Ekwo ya ba da umarnin ne a ranar Litinin bayan da Okorocha, Chinenye da kamfanoni biyar suka gurfana a gaban kuliya bisa zarge zarge 17 na halasta kudaden haram da EFCC ta shigar.
Mai shari’a Ekwo ya dage ci gaba da sauraren karar Okorocha da Chinenye har zuwa ranar Talata.
Kamfanoni biyar da ake tuhuma sune: Naphtali International Limited, Perfect Finish Multi Projects Limited, Consolid Projects Consulting Limited, Pramif International Limited da Legend World Concepts Limited.
Idan ba a mantaba JARIDAR DIMOKURADIYYA a ranar 24 ga watan Mayu ta rawaito cewa Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, tayi ram da Rochas Okorocha, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki bayan shafe tsawon lokaci suna wasan buya da ita.
EFCC ta dauke Okorocha daga gidansa da ke unguwar Maitama a Abuja da yammacin ranar Talata 24 ga watan Mayu 2022.
Tun da farko dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta mamaye gidan tsohon gwamnan jihar Imo a kokarin da take yi na cafke shi.
An ce an jiyo karar harbe harbe a lokacin da aka kai farmaki gidan Okorocha.
EFCC ta bayyana cewa Okorocha ya tsallake belinsa na mulki da aka ba shi kuma ya ki amsa gayyatar da ta yi masa.
Ana zargin Okorocha da karkatar da kadarorin jama’a na Naira biliyan 2.9 a lokacin da yake gwamnan jihar Imo.
Hukumar EFCC ta gurfanar da Okorocha a gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja a ranar 24 ga watan Junairu, 2022.
Comments 1