Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Kawo Ƙarshen Shari’ar Sanwo-Olu Da Rhodes-Vivour
Kotun kolin kasar ta fara yanke hukunci kan rigingimun gwamnonin da suka taso daga zaben 2023.
Wani kwamitin alkalai bakwai na sauraron kararrakin zabe kan kalubalantar sakamakon zaben gwamnan jihar Legas.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnonin Kano, Bauchi, Zamfara, Plateau, Ebonyi sun isa kotun koli
Ana sa ran kotun kolin za ta yanke hukunci kan kararrakin gwamnoni bakwai da suka hada da Legas, Kano, Zamfara, Plateau, Ebonyi, Bauchi da Cross River.
Jam’iyyar Labour Party (LP) da dan takararta, Gbadebo Rhodes-Vivour, da PDP da dan takararta, Abdulazeez Adediran, na kalubalantar nasarar Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jam’iyyar APC.
Jam’iyyar LP ta bukaci kotun kolin da ta tabbatar da cewa zaben na ranar 18 ga watan Maris ya tafka kura-kurai, da rashin bin dokar zabe, inda ta kara da cewa mataimakin gwamna Obafemi Hamzat bai cancanci tsayawa takara ba.
Hakazalika, Adediran ya shigar da kararraki 34 na daukaka kara yana neman kotun kolin ta soke hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Legas da kuma kotun daukaka kara.
Sai dai lauyan Sanwo-Olu, Nas Ogunsakin, ya bukaci kotun da ta yi watsi da kararrakin, ganin cewa wadanda suka shigar da karar ba su gabatar da shaidun da za su tabbatar da ikirarin nasu ba, kuma shaidun da aka kawo ba su da kwarewa.
Hukuncin da Mai Shari’a Mohammed Garba Lawal ke karantawa yana cikin karar da dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP), Gbadebo Rhodes-Vivour ya shigar yana kalubalantar ayyana Babajide Sanwoolu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zaben.