Yanzu-Yanzu: Kotun koli ta tabbatar da Uba Sani a matsayin zababben gwamnan Kaduna
A ranar Juma’a ne kotun koli ta tabbatar da zaben gwamna Uba Sani na jihar Kaduna.
Kotun kolin ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna Isah Ashiru suka shigar kan zaben Sani.
KARANTA WANNAN LABARIN:Tinubu ya gana da jiga-jigan Jam’iyyar APC na Kano bayan shan kaye kotun koli
DAILY POST ta ruwaito cewa an yanke hukuncin bai daya kuma ba a bayar da umarnin biyan wani kuɗi ba.
A yanzu haka dai kotun koli tana yanke hukunci na karshe kan rikicin zaben gwamnoni a jihohi 13 da suka hada da Delta da Kebbi da Nasarawa da Delta da Ogun da Gombe da dai sauransu.
A wani labarin kuma:Da Dumi-Dumi: Kotun Koli ta Tabbatar Da Zaben Gwamna Abiodun
Kotun koli, a ranar Juma’a, ta ki soke zaben gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe.
A wani mataki na bai daya da kwamitin mutum biyar ya yanke, kotun kolin ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta Mohammed Barde suka shigar na kalubalantar sakamakon zaben gwamnan da aka gudanar a jihar a ranar 18 ga watan Maris. 2023.