Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023.
Ya bayyana hakan ne a garin Awka yayin da yake jawabi ga sarakunan gargajiya da shugabannin al’ummomin 181 na jihar a gidan gwamnatin jihar dake Awka.
“Na zo ne domin in sanar da ku aniya ta, na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023. Ina bukatan goyon bayan ku, ”in ji shi ga sarakunan.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Obi zai bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar shugaban kasa a hukumance ne a ranar Juma’a.
Wannan shine karo na farko da Obi zai yi magana a bainar jama’a game da aniyarsa ta tsayawa takara a 2023.
“Dalilin da ya sa na kira ku, shi ne don in sanar da ku a hukumance cewa ina neman shugabancin Najeriya a bababn zaben shekarar 2023.