Paris Saint-Germain ta cire Kylian Mbappe daga ziyarar da za ta yi zuwa kasar Japan.
Zakarun Ligue 1 yanzu sun sanya dan wasan mai shekaru 24 a duniya a kasuwa.
KARANTA WANNAN: Musaya: Man Utd Ta Sayi ‘Yan Wasa Uku, Yayin Da Dan Wasan Gaba Ya Bar Old Trafford
Fabrizio Romano wanda ya kasance kwararre a harkokin musaya ne ya bayyana hakan.
“An bar Kylian Mbappé daga cikin ‘yan wasan Paris Saint-Germain don rangadin kakar wasa a Japan.
“PSG ta yanke wannan shawarar ne a daren yau juma’a.
“Ku fahimci PSG tayi la’akari da Mbappé A MATSAYIN NA SAYARWA,lamarin ya fara daga yau.
“Paris Saint-Germain tana jin Kylian Mbappé yana son barin matsayin kyauta a shekarar 2024 – duk da bai yi magana da kowa ba tukuna duk da sanarwar jami’an Al Khelaifi.
“PSG ta yanke shawarar fitar da Kylian daga yawon shakatawa na Japan,” Romano ya wallafa a shafinsa na Twittya a daren yau Juma’a.
A wani labarin kuma, Musaya: Man Utd Ta Sanar Da Barin Onana Daga Inter Milan
Manchester United ta sanar da daukar Andre Onana a hukumance kan tsabar kudi fam miliyan 47.1 daga Inter Milan.
Onana ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar da Red Devils tare da zaɓin ƙarin shekara.
Dan wasan na Kamaru zai maye gurbin David De Gea wanda yanzu ya zama dan wasa kyauta bayan ya bar Old Trafford.
Da yake magana bayan bayyana shi, Onana ya ce: “Zuwa Manchester United babban abin alfahari ne kuma na yi aiki tukuru a rayuwata don isa wannan lokacin, na shawo kan cikas da yawa a hanya.”