- Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya rusa majalisar ministocinsa.
- Shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Hakeem Muri-Okunola ne ya sanar da hakan a ranar Laraba 24 ga watan Mayu.
- Sanwo-Olu da mataimakinsa Obafemi Hamzat zasu sha rantsuwa a ranar 29 ga watan Mayu a wani sabon wa’adi na shekaru hudu
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya rusa majalisar zartaswarsa gabanin bikin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, 2023,Punch ta rawaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-yanzu: Ganduje Ya Rushe Majalisar Zartarwar sa
A ranar 29 ga watan Mayu ne za a rantsar da Sanwo-Olu da mataimakinsa Obafemi Hamzat a wani sabon wa’adi na biyu na shekaru hudu.
Shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Hakeem Muri-Okunola ne ya sanar da hakan a ranar Laraba ta hanyar wata takardar sanarwa mai lamba 046.
A wani labarin kuma, Kungiyar Gwamnonin Najeriya Ta Yi Sabon Shugaba
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya zama sabon shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF). Kamar yadda Chennels TV ta ruwaito.
Abudlrazaq ya maye gurbin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto wanda wa’adin aikinsa zai cika a ranar 29 ga watan Mayu.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Tambuwal ya sanyawa hannu a karshen taron gaggawa na gwamnonin jihohin kasar nan karo na 7 da suka gudanar a daren ranar Talata a Abuja.