Sarkin Moriki na jihar Zamfara, Alhaji Samaila Ari ya rasu.
Daya daga cikin iyalansa, Alhaji Hassan Salihu Moriki ne ya sanar da rasuwar sarkin.
Marigayi mai daraja ta biyu mai shekaru 73 ya rasu ne a wata cibiyar kula da lafiya dake Kaduna a ranar Litinin da ta gabata bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Ya bar mata daya da ‘ya’ya biyar (maza biyu da kuma mata uku).
Za a yi Sallar jana’izarsa a yau Talata da karfe uku na rana a fadar Sarkin da ke garin Moriki a karamar hukumar Zurmi ta jihar.
Kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da gwamnatin jihar ta fitar kan rasuwar marigayi Sarkin har zuwa lokacin hada wannan rahoto.