- A yanzu haka dai shugaba Bola Tinubu yana ganawa da shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa a fadar shugaban kasa dake Abuja.
- Ganawar dai na zuwa ne sa’o’i 24 bayan Tinubu ya umarci DSS da ta bar ofishin hukumar EFCC dake Ikoyi.
- Ana danganta ziyarar Bawa da ce-ce-ku-cen dake tsakanin Hukumar EFCC da DSS.
A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu yana ganawa da shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed Bawa a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa dake Abuja.
Ganawar dai na zuwa ne sa’o’i 24 bayan Tinubu ya umarci DSS da ta bar ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa dake Ikoyi.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: NNPC Ya Tabbatar Da Karin Farashin Famfo Na Man Fetur
Bawa wanda ya isa fadar Villa da misalin karfe 2 na rana, an kai shi harabar ofishin shugaban kasa.
Duk da cewa har yanzu ba a bayyana makasudin taron ba, amma ana iya danganta shi da ce-ce-ku-ce tsakanin Hukumar EFCC da DSS.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Tinubu, a ranar Talata, ya umurci DSS da ta gaggauta ficewa daga ofishin EFCC na Ikoyi da ke Legas.
Shugaban ya bayar da umarnin ne a lokacin da aka kai rahoton cewa jami’an DSS sun kai farmaki ofishin EFCC da ke kan titin Awolowo, Ikoyi a ranar Talata, inda suka hana jami’an hukumar shiga wuraren aikinsu.
Jami’an DSS sun kai farmaki ofishin ne da misalin karfe 7:00 na safiyar ranar Talata inda suka ki fita duk da tattaunawar da aka yi tsakanin jami’an hukumomin biyu.
Wannan ci gaban na ranar Talata ya biyo bayan cece-ku-ce tsakanin hukumar DSS da EFCC kan mallakar ginin.
Hukumar EFCC ta bayyana kaduwarta da yadda ‘yan uwnta jami’ai suka hana jami’anta shiga ofishinta na Legas.
Sai dai hukumar ta DSS ta musanta ikirarin, inda ta bayyana shi a matsayin “ba gaskiya bane.”
Da yake mayar da martani game da ci gaban da aka samu a yammacin ranar Talata, shugaban ya ce “Idan da akwai batutuwan da ke tsakanin muhimman hukumomin gwamnati biyu, za a iya warwari shi cikin ruwan sanyi.”
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Wani Sanata Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
Sanata mai wakiltar Edo ta Kudu a majalisar dattawa ta tara, Matthew Urhoghide, ya fice daga jam’iyyar PDP, kamar yadda Punch ta rawaito.
Murabus din Urhoghide na kunshe ne a cikin wata wasika da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, wanda ya jagoranci zaman majalisar a ranar Laraba ya karanta.