Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta lallasa kasar Saliyo da ci 2-1 a wasan farko na neman tikitin shiga gasar cin kofin Afrika (AFCON) da suka fafata a filin wasa na Mashood Abiola ranar Alhamis.
Jonathan Morsay ne ya fara cin kwallo a minti na 11 da fara wasa, sai dai kuma dan wasan Everton Alex Iwobi ya yi gaggawar ramawa Najeriya kwallo a minti na 16 da fara wasa.
Victor Osimhen ne ya kara kwallon daga bugun daga kai sai mai tsaron gida da Moses Simon ya yi a minti na 41 da fara tamaula, lamarin da ya sa ‘yan Najeriyar suka samu dukkan maki uku.
Da wannan nasarar Najeriya ta zama ta biyu a rukunin A da maki uku a wasa daya.
Guinea-Bissau ce ta daya a kan teburi, Najeriya, ta nada ragowar kwallaye 4 a raga bayan ta doke Sao Tome and Principe da ci 5-1 a karawarsu.
A wani labari Kuma na daban
Da Dumi-Dumi: Osinbajo ya yi martani kan nasarar da Tinubu ya samu a zaben fidda gwani na jam’iyar APC
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya taya tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu murnar nasarar da ya samu a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Osinbajo ya kuma taya shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugabannin jam’iyyar APC murnar gudanar da babban taro na musamman cikin nasara.
Mataimakin ya ce shekaru da dama, Tinubu ya nuna kishin kasa, jajircewa a wajen gina kasar nan.
Osinbajo a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis ya bayyana cewa babban gudunmawar da shugaban jam’iyyar APC ya bayar ga dimokuradiyyar Najeriya da ci gaban da ta samu ya fito fili.
“Kwarewar sa na da matukar muhimmanci a ci gaba da kokarin da jam’iyyarmu ke yi na samun kwanciyar hankali da wadata a Najeriya,” in ji shi.
Osinajo ya bukaci ‘yan jam’iyyar APC da su hada kai su marawa Tinubu baya domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben 2023.
Sanarwar ta kara da cewa, “Dole ne mu kasance mun hade Kai wuri guda, wajen cimma burinmu a matsayin jam’iyya don gina kasar da za ta iya samar da ingantacciyar rayuwa ga daukacin al’ummarmu”.